Okonjo Iweala ta gana da Hillary Clinton (Hotuna)
Tsohuwar Ministan kudi ta Najeriya Dakta Ngozi Okonjo-Iweala ta burge mutane da yawa musammam ‘yan Najeria da ke Amurka, sakamakon ganawar da ta yi ‘yar takarar shugaban kasa a jam’iyyar Democrat, Hillary Clinton
Tsohuwar Ministan a zamanin mulkin Goodluck Jonathan, ta yada wani hoto da ta dauka tare da Hillary Clinton ne a ranar Asabar 6 ga watan Agusta 2016 a shafinta na sada zumunta da muhawara na Twitter a Intanet.
Dubban ‘yan Najeriya ne tsohuwar ministar ta burge da irin ganawar da ta yi da ‘yar takarar shugabancin kasar a karkashin jam’iyyar Democrat a Amurkan. Ko da ya ke wasu ma tambayar sahihancin ganawar suke yi dakuma hotunan da ministan da ‘yar takarar
Da ya ke shan koko daukar rai ne, wasu ‘yan Najeriyar da yawa da mai ra’ayin cewa, abokin adawarta Donald Trump na jamiyyar Republican ne ‘yan Najeriyar ya kamata su marawa baya, duk da ka-ce-na-ce da ya ke janyowa a dandalin sada zumunta da muhawara a intanet.
Bincike ya nuna cewa tsohuwar Ministan na da kyakkyawar alaka da iyalin Clinton, ga misali, sun taba gayyatarta wani taro kan matsalolin kudi na kasa-da-kasa a New York ta Amurka a shekarar 2015 da kuma 2014.
Dakta Ngozi Okonjo-Iweala tsohuwar ministan kudi kuma shugabar babban kwamitin ta kula da arzikin kasa a Najeriya, babbar darakta ce a Bankin Duniya kafin Cif Obasanjo ya ba ta mukamin minista a farkon mulkinsa, daga baya ta ci gaba da rike mukamin a zamanin Goodluck Jonathan.
Asali: Legit.ng