Ba takalmin zinari ne gaba na ba -Inji Etebo

Ba takalmin zinari ne gaba na ba -Inji Etebo

Dan wasan gaban tawagar kungiyar kwallon kafar kasar Najeriya Oghenekaro Etebo ya bayyana cewa ya fin burin kasar Najeriya ta maimata abunda ya faru na nasarar da ta samu a gasar Atlanta 96 fiye da shi samun takalmin zinarin sa.

Dan kwallon wanda kuma dan kulob din CD Feirense ne ya zura kwallaye har 4 a wasan da Najeriyar ta buga da kasar Japan a jiya Juma'a. Da yake zantawa da manema labarai, dan kwallon Etebo yace: "koda zan fi kowa cin kwallo a gasar idan dai har bamu lashe gasar ba to kwallayen basu da wani anfani. Ni ba haka nike so ba."

Ba takalmin zinari ne gaba na ba -Inji Etebo

"Tabbas akwai dadi idan mutum yana taimakawa kungiyar sa musamman ma wajen zura kwallaye to amma ni kofi nafi son mu lashe ba wai cin kwallaye kadai ba." Dan wasan kuma daga bisani sai ya bukaci yan Najeriya da su ci gaba da taimakamasu da addu'a da kuma goyon baya don hakan zai kara masu kwarin gwiwa.

A bangaren sa kuwa, mai horar da tawagar Siasia cewa yayi: "Wasa daya ne fa mukayi nasara. Ba zamu bari ba wannan nasarar da muka samu ta sa mu shagalta ba. Zamu cigaba da aiki tukuru dan ganin mun lashe kyautae zinarin gasar."

Kasar Najeriya zata sake karawa ne da kasar Sweden a wasan su na gaba a ranar Lahadi 7 ga watan Agusta da karfe 11na yamma a agogon Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel