Mabiya Zakzaky sunyi magana akan shugaban su.
- Al-jazeera sun Sami daman tattaunawa da mabiyan Sheik Al-zakzaki, wanda har yanzu yana tsare a hannun DSS.
- Daya daga cikin mabiyan na Shi'a tace, shugaban na shi'a kamar ubane a wurinta.
- Tace taso ace dan shi'a ya zama shugaban kasar Najeriya mai zuwa.
Mambobin Shi'a ta Najeriya {IMAN} sun fito kan manya-manyan hanyoyi babban Birnin Najeriya Abuja satin daya gabata dan neman a saki shugaban su Sheik Ibrahim Alzakzaki.
Matasan yan matan dai suna kuka, su kuma samarin suna dauke da takardu a hannun su. Zakzaki da matarsa suna ajiye a wani wuri da ba'asan ko ina neba wanda ma'aKatan tsaro na farin Kaya suke kira da "boyayyen gurin ajiya" tun watan disamba 2015.
An kama dai shugaban na shi'a ne bayan gwabzawar da sukayi da sojoji na tsawon kwana uku, wanda ake zargin sojojin sun kashe daruruwar yan kungiyar a birnin zariya dake jahar kaduna. Hafsat Hussain yar shekara 14 ta bayyana ma Al-jazeera wani irin mutum ne shi ainihin shugaban su Alzakzaki da kuma yadda akayi ya fahimtar da ita akan akidar na shi'a.
Ta bayyana cewar " sheik Alzakzaki malami ne kuma uba ne a Gare ni domin kuwa ya koyamin yadda zan bautama Allah daya halicceni, ya kuma koya min yadda zan yima Allah biyayyah, kuma ya maida rayuwa mai kyau, abunda zan iya cewa shine Sheik Alzakzaki mutum ne nagari, mutane da yawa fahimceshi ba, wasu mutane suna cewa yan shi'a ba musulmai bane inda suke cewar wai suna amfani da hijabi ne kawai domin su rufe tsaraicin su kawai, kuma sunce bama bauta ma Allah.
KU KARANTA : Muna cigaba da tsare El-Zakzaky ne da yardar sa -DSS
Gwamnatin Najeriya basu son shi,a suna harin mu, wani lokaci inajin tsoro bana samun natsuwa, kamar jiya da mukayi zanga zanga yadda yan sanda suke mata tsawa baidace ba. Inaso na zama likita saboda na na taimaka ma shi'a dakuma mutanen duniya, inason naje Iran naji abunda ke faruwa a Iran domin inabin abinda ke faruwa acan,duk da ba kowane lokaci ba,amma ina sanin abubuwan da ke faruwa ta Jarida.
Ina so wani dan shi'a ya zama shugaban kasar Najeriya.
Asali: Legit.ng