Ga fa hotunan wata mata maishekaru 59 da ta samu ciki
So dayawa mukanyi gamo da labarai masu sosa zuciya da kuma ban al'ajabi. Tabbas idan har da ranka to kana da sauran kallo kamar dai yadda masu iya magana ke cewa.
Kamar dai yadda kowa yasani ribar aure itace haihuwa. So dayawa aurarraki ke mutuwa saboda rashin haihuwa. Tabbas duk wanda yayi aure to nada burin shima ace wata rana gashi ya samu nashi ko tashi dan ko diyar.
Wasu ma'auratan da yawa kuma sukan sha wahala sosai wajen neman haihuwar kafin su samu. Wasu ma har sai sun hakura sun fawwala wa Allah komai sannan kawai sai su samu haihuwar. Tabbas samun haihuwa baiwa ce daga Allah.
Masu karatu tabbas labarin wata Claudette Cook's zai kayatar da ku. Ita dai Cook shekarar ta 59 sannan ta samu ciki sabanin hadda al'adar dan adam take. Cook ta auri mijin ta ne kusan shekaru 9 da suka wuce amma bata samu haihuwa ba duk da cewar ita ma bata neman haihuwar saboda tsufa.
Duk da haka kuwa, ai ance ikon Allah ya wuce mamaki sai gashi ta su ciki har ya girma kuma likitoci sun tabbatar mata da cewa yan biyu ne take dauke da su. Abu mafi sha'awa kuma shine yadda take cikin koshin lafiya.
Asali: Legit.ng