Rio Olympics: Dalilin rashin hatimin NFF a rigar 'yan kwallon Najeriya

Rio Olympics: Dalilin rashin hatimin NFF a rigar 'yan kwallon Najeriya

Sabuwar rigar yan kwallon Najeriya na Super Eagles dai bata dauke da hatimin hukumar kula da kwallon kafar kasar nan watau NFF a jikin ta. Wannan ne ma yasa masoya kwallon kafa suke ta tambayar ko meye dalilin hakan.

Kamfanin jaridar goal.com dai ya bayyana cewar kamfanin da yake yi wa kasar Najeriya riguna watau Nike yace kwamitin kula da gasar ta Olympics watau International Olympic Committee (IOC) shine ya hana a sanya hatimin. "A wannan gasar ta Olympics, kasashe ba zasu sa hatimin su. Wata sabuwar dokar IOC ce ta umurci hakan." Inji mataimakin kamfanin Nike din na Afrika Tina Salman.

 

Rio Olympics: Dalilin rashin hatimin NFF a rigar 'yan kwallon Najeriya

"Sabuwar dokar ta IOC ta bada damar saka tutar kasa ne kawai mai girman 25cm2 don gudun kar a kacalcala rigar da zane." Kamar dai yadda yake a cikin sabuwar dokar. "Dokar ta kuma ce za'a iya sa tutar kasa a jikin hannun rigar amma shima kar ya wuce girman 25cm2".

"Har ila yau dai za'a iya sa tutar kasa a kusa da kwalar riga amma karama wanda ba zai wuce girman 15cm2 ba."

Su dai kungiyar ta Najeriya ta lallasa kasar Japan ne da ci 5 - 4 a wasan da suka yi na farko a garin Manaus.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng