Abunda Pogba ya fadawa Ferdinand yayin da ya bar Man Utd a 2012

Abunda Pogba ya fadawa Ferdinand yayin da ya bar Man Utd a 2012

Tsohon dan wasan kungiyar Man utd na baya Rio Ferdinand kuma wanda ya buga wasa tare da matashin dan kwallon nan Pogba a kungiyar ta Man utd ya bayyana cewa Pogba din ya taba fadamasa cewar zai bar kungiyar ne don kwadayin zama shahararren dan kwallon duniya wata rana. Pogba din ya ci gaba da fada masa cewar zai bar Man utd din ne don ya samu damar buga kwallo a wani kulob din.

Haka ma Rio Ferdinand din ya ce shi a nashi ra'ayin dan wasan ya cancanci kudin da aka sa masa na £100m a kokarin da kulob din yakeyi don ganin yadawo da shi. A cewar sa: "Na taba yin magana da Paul. Ina ganin ya cancanci kudin sa. Ba wai yawan kudin za'a kalla ba, kwallon da zai buga idan ya zo za'a kalla."

Abunda Pogba ya fadawa Ferdinand yayin da ya bar Man Utd a 2012
Rio Ferdinand duringHausa

Ferdinand din ya cigaba da cewa: "Ni nasan Paul. Mutum ne mai son kwallo kuma yana kara kwarewa a kullum. "A lokacin da zai bar kungiyar ta Man utd ya shaida mani 'ina son in zama gwarzon dan kwallon duniya', kuma a tunani na yana kan hanyar zama hakan." Idan dai har cinikin ya tabbata, Pogba zai zama dan kwallo na farko da aka taba siye da wadannan makuden kudin da suka kai £100m a tarihin kwallon kafa a duniya. Ana sa ran dai za'a kammala cikikin matashin dan kwallon mai shekaru 23 a duniya daga kulob din Juventus zuwa Man Utd.

Asali: Legit.ng

Online view pixel