Tsohon dan kwallon Najeriya Ogaba ya mutu

Tsohon dan kwallon Najeriya Ogaba ya mutu

Wani tsohon dan kwallon kasar Najeriya wanda kuma ke zaman wanda yafi kowa karantar shekaru da ya taba buga ma kasar kwallo a ajin yan kasa da shekaru 16 aduniya ya mutu.

Shi dai wannan dan wasan yana cikin tawagar yan wasan kasar da suka wakilci kasar a gasar cin kofin duniya na yan kasa da shekaru 16 wanda akayi a kasar Canada a shekarar 1987 inda kasar Soviet Union ta fidda kasar ta Najeriya a gasar.

Ogaba din dai ya buga wa kungiyoyi da yawa kwallo wadanda suka hada da Boldklub Hostelbus, Desportivo Club Beja dama Lokeren duk a kasar turai.

Tsohon dan kwallon Najeriya Ogaba ya mutu
Francis Achi announces Peter Ogaba's death

Shi dai mamacin ya mutune a gidan sa dake garin Abuja bayan yayi fama da gajeruwar rashin lafiya.

Kafin mutuwar tasa dai yana zaman mai horarwa ne ga

Wani wanda ake kira da Francis Achi shine ya sanar da mutuwar dan wasan kafin daga bisani hukumar kula da harkokin kwallon kafa ta kasa watau NFF suma su bayyana bakin cikin su game da mutuwar ta asusun su na sadarwar zamani a tuwita.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng