Hukumar NDLEA ta kama mai fataucin kwayoyi
Hukumar yaki da fataucin kwayoyi ta NDLEA ta cafke wani mutum dan shekaru 32 mai suna Vincent Chidiebere a garin Awka na jihar Anambra dauke da muggan kwayoyi da kudaden su ya kai naira biliyan 1 da miliyan 78.
An kama mutumin ne da kwayar methamphetamine da nauyin ta ya kai kilo 25, bayan samun labarinsa da hukumar tayi.
Kwamandan hukumar NDLEA na jihar Sule Momodu ya bayyana cewa kawayar methamphetamine na daya daga cikin kwayoyi masu hatsari a duniya wanda ka iya salwantar da rayuwan mai mu’amala da ita. Sa’nnan kuma kwayar na iya cutar da al’ummar dake hada ta, sobada sinadarin kwayar ka iya bata iskan da jama’a ke shaka.
Kwamandan yace kingin sinadarin kwayan dake samuwa bayan an kammala hada asalin kwayar yafi hatsari, kuma yafi illata masu mu’amala da ita, wanda zai iya samar wa jama’a cutar daji wto cancer, hatta yayan dake ciki bai bari ba.
Asali: Legit.ng