Rashin bacci na iya kashe ‘ya mace - Malaman Kimiya
Bacci abu ne mai muhimmanci a kan lafiyanmu. Amma shin mata na bukatan bacci fiye da maza? Kimiya ta bayyana haka,kuma ga dalilin.
Shin ta wani dalili mata suka fi bukatan bacci?
Mata sun fi fasaha, shin dalilin ke nan ? Amma ba haka bane , ga abin da malaman kimiya suka ce shine dalilin nan: kwakwalwan mace ya karfi fiye da namiji . zasu iya abubuwa iri iri a lokaci guda , kuma suna iya amfani mafi akasarin kwakwalwan su fiye yanda maza ke yi.
Saboda haka, sun fi bukatan bacci saboda hutawa, ga abinda wani masanin bacci ya fada.
“Daya daga cikin muhimmancin bacci shine a bari kwakwalwa ta huta kuma tayi nishadi. Dangane da yanda kake amfani da kwakwalwan ka da rana, haka zata bukaci hutawa da dare, kuma haka zaka bukaci bacci.. Amma, zancen yawan bacci ne bashi da muhimmanci a yanzu. Mata na bukatan baccin mintuna 20 fiye da maza a kowani rana . kuma yanada kyau ga jikin dan Adam. Kuma mazan da ke aikin kwakwalwa sun fi bukatan bacci fiye da masu aikin karfi.”
aKU KARANTA : Gwamnati ta raba awaki 720 ga mata, karfafa gwuiwa ne ko….?
“A wata Ilimi mai ban shaawa shine maza sunfi hade hade a cikin kwakwalensu, amma mata sunfi hade hade a ciki. Shi yasa maza sukafi mayar da kai wajen abubuwan da sukeyi kuma mata ke iya raba kansu wajen yin abubuwa daban daban a lokaci guda. Zamu hada kwakwalwa da mota. Na mata ya fi gudu, amma na maza ta fi iya daukan kaya masu nauyi. Kwakwalwan mata karami ne kuma yafi saurin rugujewa. Shi yasa sukafi bukatan bacci.”
Saboda haka, rashin bacci na iya kawo mugun sakamako ga mata,fiye da maza. Rashin bacci na iya canza rayuwan mutum, kuma na iya kashe mace.
Asali: Legit.ng