Mace ta haifi yan biyar

Mace ta haifi yan biyar

Wai! Ya za’a ga girman cikin mace mai dauke da yan biyar? An samu wata mata da ta haifi yan biyar a lokaci daya, kuma duk masu cikakken koshin lafiya.

Mace ta haifi yan biyar
uwar da yayanta

A kowane shekara ana samun haihuwar yan biyar guda goma a kasar Amurka. Wadannan ma’auratan sunyi matukar samun sa’a, tabbas wannan mata ta cancanta a jinjina mata yadda ta dauki cikin yayanta biyar sannu a hankali cikin farin ciki. Gaskiyar magana shine, matar ta shiga cikin hatsarin samun matsalar haihuwa daga kowanne daya daga cikin jariran. Wannan mata jaruma ce. Ta yi fama da wahalhalu iri iri a yayin da take dauke da cikin.

Mace ta haifi yan biyar
matar a asibiti

Daga kallon cikin nata, za’a iya gane cewa matar ta wahala saboda ganin zanen ciwo a cikin da ya samu dalilin daukan yaran da tayi. Sunan matar Guillermina, kuma yar shekara 32 ce. Uwar jariran tayi dawainiya da cikinnasu na tsawon sati 32. Wato sati daya kenan kari akan lokacin da cikin yan biyar ke kaiwa. Da kanta taje dakin haihuwa, inda likitoci takwas suka duba ta har ta haihu cikin koshin lafiya. Matar ta haifi maza biyu da mata uku, dukkanin su na nan cikin cikakken koshin lafiya.

Sunayen jariran sune Esmeralda, Fatima, Marissa, Fernando da Jordan. Iyayen jariran sunyi murna matuka, kuma sun hada gagarumin biki don murnar zagayowan ranar haihuwansu. A gaskiya wannan matar tayi nuna juriya sosai wajen dawainiya da cikin jariranta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel