Wata Bayaraba ta kirkiro agogo mai yarbancin (Kalli Hotuna)
Wata bayaraba mai suna Moyinoluwa Adeyemi ta kirkiro wata fasahar wayar Android ta agogo da take fadin lokaci cikin harshen yarbanci.
Ita dai Moyinoluwa Adeyemi ta kammala digirin ta ne na fasahar kimiyyar na'ura mai kwakwalwa watau 'Computa Science' daga jami'ar Obafemi Awolowo sannan ta je wata makaranta ta Swifta System don karin ilimi. Ita dai wannan mata tana kuma cikin wasu gun-gun yan Najeriya da suke da alaka da kamfanin fasahar zamanin nan ta Google.
Moyinoluwa ta bayyana cewar ta samu kwarin gwuiwar yin wannan fasahar ne a wani lokaci a can baya da ta kalli agogo tana tunanin ya za'ayi agogon ta rika fadin lokutta a cikin yarukan mu na gargajiya. A cewar ta wannan ne ma ya bata kwarin gwuiwa a yayin da ta ci gaba da bincike don ganin hakar ta ta cimma ruwa.
Ya kuke ganin wannan fasahar?
Asali: Legit.ng