An kama kanana yara barayi masu satan kwamfuta

An kama kanana yara barayi masu satan kwamfuta

Hukumar yansanda ta jihar Legas ta cafke wasu yara kanana da laifin kutsa kai wata makaranta a unguwar Somolu dake jihar, suka yi sata.

An kama kanana yara barayi masu satan kwamfuta

Wadanda ake zargin sun hada da Yinka Adesola dan shekara 19 da Ahmed Olaleye dan shekara 17, tare da wasu mutum hudu sun shiga marantar sakandari ta Angus memorial, A cewar jaridar Punch. Sauran mutunae hudu da ake zargi da satan sun hada da Lukman Sokoya, Ismaila Adebowale, Wasiu Adejare da Ramon Mukaila, kuma an cafke su ne a ranar Laraba inda ake zargin su das ace na’ura mai kwakwalwa wato kwamfuta, na'urar daukan hoto, kwamfutan tafi da gidanka, da kuma na’urar buga takardu duk mallakan makarantar.

An samu labarin jami’an tsaro na ‘Rapid Response Squad-RRS’ na jihar Legasa sun kwato wasu daga cikin kayayyakin da barayin suka sata. Majiyarmu ta fadi “jami’an tsaro na RRS sun samu labara daga jama’a cewa daya daga cikin barayin na boye a titin Awoseni. Bayan an kama shi ne sai ya fada mana shi ne ya siya daya daga cikin na’uran kwamfutan tafi da gidanka da aka sata. A haka ne muka kama shi tare da sauran mutum biyar da ake zargi.”

A maganganu da Adesola ya fada ma yan sanda, ya karyata zargin da ake musu na kutsa kai cikin makarantar, inda yace wani ne Olaleye ya ajiye kayan a dakinsa.

Yace “ na san ina da abokai yan iska wadanda zasu iya sani cikin matsala. Na baiwa Olaleye masauki bayan wadanda suke tare da shi sun tashi daga gidansu dake Somolu. Na taimake shi ne ganin shi yana kasa dani a makarantar sakandare. “kwanaki kadan bayan ya dawo gidana, sai makwabtana suka fara rasa wayoyinsu da kudadensu. Daga baya muka gane shine ke sace sacen, daga nan iyayena suka nemi in kore shi, kuma na aikata hakan.

“amma kafin wannan lokacin, ya kawo ajiyan kwamfuta guda bakwai, na’urar daukan hoto, da kuma na’urar buga takardu a dakina. Duk da cewa nag a sunan makaranta akwan kayayyakin, amma sai nayi tunanin tun da yana kai ziyara makarantar akai akai, kila shi yasa suka bashi kyauta. Ban san cewa satosu yayi ba.

“bayan kwana biyu da naga bana ganinsa, sai nayi yunkurin siyar da kayayyakin. Na siyar da wasu daga cikinsu, amma wasu na dakina, na baiwa abokai na wasu siyar min dasu.

Jami’i mai magana da yawun hukumar yan sanda na jihar Dolapo Badmus ya tabbatar da kame masu laifin “hukumar zata tabbatar da an fatattaki masu aikata miyagun laifi daga jihar, za’a gurfanar da masu laifin a gaban kotun da zarar an karkare bincike.”

A wani labari kuma, an kama wasu kananan yara yan fashi da yan kungiyar asiri a unguwar agege da Ikeja a jihar Legas. Wadanda aka kama sun hada da maza 18 da mata 4, kuma an kama su ne unguwar agege kamar yadda jami’an tsaro suka bayyana. Gungun farko da aka kama na mutum takwas n, kuma suna da shuwagabanni mutum 2 masu suna Babatunde da Tayo masu shekaru 15.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng