Yunwa na kashe mutanen da ke tsare a sansanin Boko Haram
–Maza,mata da yara na mutuwa kulli yaumin a sansanin Boko Haram a dajin Sambisa
–Wani wanda ya tsira ya siffanta hali da yan Boko Haram din ke ciki a sansanin su.
Daruruwan maza,mata da yara marasa hakki da yan Boko Haram suka tsare a dajin sambisa na mutuwa domin yunwa mai tsanani.
Wata sabuwar labari da aka samu akan al'amarin daga harshen wani wanda ya tsira daga hannunsu . Mutumin wanda an sakaye sunanshi ya ce mutane da yawa na mutuwa kulli yaumin sanadiyar rashin abinci da yunwa a cikin dajin Sambisa, kuma yana kira rundunar Soji su karfafa tsirato mutanen.
Game da cewar wanda ya tsiran, shugabannin Boko Haram da matansu na rayuwa cikin hanyoyi karkashin kasa ne. An samu rahoton majiya cewa yan kungiyar boko haram din sun tafi da mata da yara bila adadin zuwa kasar Chadi.
KU KARANTA : An sace kayan masarufin ‘Yan gudun hijra a Adamawa
Ku tuna cewa a makon da ya gabata, diraktan yada labarai da hulda da mutane na rundunar Sojin kasa, Kanal Sani Usman Kukasheka,ya sanar da cewan an rigaya da an fitittiki yan Boko Haram a sansanin su a fadin yankin Arewa maso gabashin kasa baki daya.
Asali: Legit.ng