Ya saki matarsa ta shekaru 21 don bata iya girki ba

Ya saki matarsa ta shekaru 21 don bata iya girki ba

Wani mutum dan shekaru 54 ya roki wata kotun gargajiya dake igando da ta warware aurenshi da yayi na soyayya da matarsa wanda suka kwashe shekaru 21 suna tare saboda rashin girki na matan.

A shari’ar da Alkalin kotun mai shara’a Agegboyega Omilola ya yanke, yace mutumim mai karar ya tirjiya sosai kan atafau sai an raba aurennan duka da kokarin sulhu da kotu tayi don ceton auren. Daga nan ne fa kotun da yane cewa “daga yau babu aure tsakanin Ashimiyu Abiodun da Aisha Abiodun; don haka ma’auratan sun tashi daga matsayin mata da miji.

“dukkaninsu su biyu za su iya kama gabansu ba tare da cin mutuncin juna ba,” inji alkali Omilola.

Mutumin yace “mata ta bata iya girki ba, koda yaushe ka dandana abincin ta sai kaji ba dadi. Duk lokacin da tayi girki kuma nayi korafi, sai tace wai inje in girka da kaina. Daga nan ne na fara girka abincina da kai na, saboda idan da na cigaba da cin grikinta, toh da nayi rashin lafiya.

“matata kazama ce; bat a sharan gida balle ma wanke shi, ko ina a gidan wari yake yi. Si ta tara kwanukan abinci har na kwana hudu kafin ta wanke, kuma ma ni ke wankewa.

“sai Aisha ta fita gida tun juma’a bata dawowa sai yammacin Lahadi, idan ko ranakun aiki ne, karfe 7 na safe take barin gida, bata dawowa sai tsakar dare, ban taba mata magana ba. Ta sanya yayana sun juya mini baya, sun dai girmama ni, kuma bata bari in kwabe su idan sunyi ba dai dai ba. “a lokutta da dama, matata da yaro na na fari sais u hade kais u yaga min riga kan wai ina son in ladabtar da yaron kan laifukan da yake aikatawa.” Inji shi.

Ita ko matar tasa yar shekaru 46 Aisha Abiodun cewa tayi “ban san dalilin da yasa mijina ya daina cin abinci na ba, ina iyakan kokarina in bashi abinci mai kyau, amma kullum sai ya dinga korafi wai abincina ba dadi. Ni ba kazama bace tun da ina share gidana kullum kullum.” Daga karshe ta bukaci kotun da tayi watsi da bukatun mijin nata, kada a kashe aurensu domin haryanzu tana son abinta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng