Tarihi: Yarjejeniyar Hudaibiyya 632

Tarihi: Yarjejeniyar Hudaibiyya 632

A baya Legit.ng ta wallafa wata wasika da wani Abdulrahman Mohammed wanda ya yi ridda ya rubutawa mabiya addinin Krista, a inda wasikar ta yadu a shafukan intanet, kuma ‘yan Najeriya suka tofa albarkacin bakinsu, ga raddi don warware zare da abawa;

Tarihi: Yarjejeniyar Hudaibiyya 632
Dakin Allah Mai tsarki a Makkah

Da sunan Ubangiji,

Wannan yajejeniya ce tsakanin Muhammadu (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi), dan Abdullahi da kuma Suhayl dan Amr. Sun yarda da su ajiye makamai na tsawon shekaru 10. A tsawon wadannan shekaru, jama’arsu za su kasance cikin aminci, kuma babu wanda zai cutar da wani, sai dai amana da girmamawa a tsakaninsu. Cikin Larabawa duk wanda zai kulla yarjejeniya da Muhammadu (Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi), zai iya yin haka, haka ma da Quraishawa. Idan Baquraishe ya gudu gun Muhammadu (Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi), ba tare da izini ba, za a mayar da shi. Idan kuma na wurin Sa ne ya gudo, ba za a mayar da shi ba. Dole Muhammadu (Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya koma gida, a wannan shekara ba za yi hajji ba, shekara mai zuwa zai iya zuwa ya yi kwana 3, ba kuma tare da makami ba…”

KU KARANTA: Tarihi: Sarkin Musulmi na farko a Lagos 1895

Shekaru biyu da kulla yarjejeniyar, ‘yan kabilar banu Bakr da suka yi abota da Quraishi suka kashe wasu ‘yan kabilar Banu Khuza’a masu kawance da Musulmai, hakan ta sa Manzon Allah,(Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ba mutanen Makkah zabi na; ko su biya diyya, ko su yanke abota da Banu Khuza’ah , ko kuma yarjejeniyar Hudaibiya ta warware.

 

 

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng