Uwargidan Asari Dokubo ta rasu a hadarin mota
–Tsohon shugaban yan bindiga, Alhaji Mujahid Dokubo Asari, ya rasa uwargidan shi, Hajia Zainab Asari Dokubo.
–Alhaja Zainab ta rasu nr wata hadarin mota tare wata kawarta a hanyan Ibadan.
–Kafin rasuwar ta, ta kasance sakataren Hukumar aikin Alhazai.
–Ta rasu ta bar yara 4, Amirah, Hassan, Hussain da Osama.
Uwargidan tsohon shugaban yan bindiga, Alhaji Mujahid Dokubo Asari, alhaja Zainab Asari Dokubo ta rasu.
Jaridar Vanguard ta bada rahoton cewa ta rasu ne tare da kawar ta a wani mumunan hadarin mota da aya auku a hanyar zuwan su garin Ibadan.
Shugaban al'umman musulman jihar oyo, Alhaji Ishaq Kunle Sani , wanda ya tabbatar da rasuwan ta ya fadi a wani jawabi cewa Zainab ta kasance musulma kafin ta auri Asari Dokubo.
“Ko a hakan, ya na wuya a share wata daya bata shigo Ibadan domin wani taron musulnci ba. Ta kasance mamban kungiyoyin musulunci daban daban harda Al'ummar musulman Oluyole karkashin jagorancin imam Mudashir Bada.
“Da kyau cewa a yayinda ta ke hanyar zuwa garin da tafi so ne ta hadu da kaddaram ta. Ta bar yara hudy Hassan, Hussein, Osama da Amira. Muna rokon Allah ya karbi jihadinta a matsayin ibada ya kuma sanya ta Aljannah Firdaousi.” Alhaji sani ya fada.
Asali: Legit.ng