Abinda yasa naki zuwa Manchester United-Sadio Mane
Sabon dan wasa da kingiyar Liverpool ta siya Sadio Mane yace yafi sha’awan yin wasa a karkashin Jurgen Klopp fiye da zuwa Manchester United.
A bayabayan nan ne dai Liverpool ta siya Sadio Mane dan shekara 24 inda ya rattafa hannu a kwantaragi na shekaru masu dama akan pan miliyan 34 daga Southampton.
Rahotanni sun nuna cewa Manchester united ma ta nemi zawarcin dan wasan dan kasar Senegal din tun zamanin Luis Van Gaal har zuwa yanzu Mourinho ma ya neme shi, da aka tambayeshi dangane d United sai yace “da gaske ne, kungiyoyi da dama sun neme nib a ma Manchester United kadai ba, amma da Liverpool suka shigo, sai kawai naji ina sha’awar zuwa can, sune suka dace dani, mai horar dasu ma ya dace dani
Ya kara da cewa “liverpool babban kungiyane mai cike da tarihi, kuma taci kofuna da dama, tun da na fahimci akwai alamun zan zo nan, kuma na samu labarin koci na so na, sai nace Eh. “nayi abin da ya kamata. Na fahimci matsayin kungiyar, kuma ita ta dace da koma don cigaban kai na. abinda ya kamace ni kenan.”
Idan ba’a manta ba dai, Liverpool ta siyar da yan wasa da suka hada da Jordon Ibe, Joao Teixeira, Sergi Canos, Toure, Skrtel, Joe Allen da Jerome Sinclair. Ana sa ran shima Christian Bente zai bi su idan wani cinikin pan miliyan 20 tsakanin su da Crystal Palace ya kaya. Sa’annan kuma ta siya Sadio Mane, Joel Matip, Klavan, Joe Manninger, Giorgino Wijnaldum, Marko Grujic da Loris Karius.
Asali: Legit.ng