Karen da yafi tsawo a Duniya mai nauyin kilo 72

Karen da yafi tsawo a Duniya mai nauyin kilo 72

Ana tsammanin za’a bayyana wani kare mai suna Great Dane Major dan shekara 3 da tsawonsa ya kera na masu gidansa Brian da Julie Williams a matsayin Karen da yafi tsawo a Duniya.

Karen da yafi tsawo a Duniya mai nauyin kilo 72
karen zaune tare da masugidansa

Tsayin Karen a tsaye ya kai mita 12 kuma nauyinsa ya kai kilo 72. Ana tsammanin masu shirya kundin tarihin daniya zasu bayyana shi a matsayin Karen da yafi tsawo a duniya, sai dai masu gidan Karen Brian da Julian sunce duk da irin mugum kallon da yake das hi, Dane baya cizo, kuma yana da kirki.

Karen da yafi tsawo a Duniya mai nauyin kilo 72
Karen da yafi tsawo a Duniya mai nauyin kilo 72

Wannan babban kare yana barci na awanni 22 a kowane rana, kuma yana da katifarsa da ta kai girman ta mutum, sa’annan Karen na more abinci mai dadi, yafi kaunan cin shinkafa da kaza, kuma yana son yawatawa kusa da gidan su.

Karen da yafi tsawo a Duniya mai nauyin kilo 72
karen yana cin abinci

A sa’ilin da mai Karen Mr Williams ke bada bayani game da Karen, yace “kare ne mai kirki, jama’a na son kallon shi, sai su wuni suna wasa da shi. Yana karami muka siye shi, kuma mun dade tare da shi. Yana da daman zuwa duk inda yaso a unguwarmu, bama daure shi. Bai taba bamu matsala ba, asali ma yana jin tsoron inuwarsa, yana son yara, sa’annan yana da hakuri da saukin kulawa, yana burgemu gaskiya.

Karen da yafi tsawo a Duniya mai nauyin kilo 72

Mista Williams yace Karen nasa nada ban tsoro a fuska, amma fa akwai hakuri da saukin kai, kuma baya fushi. Masu gidansa Brian da Julian Williams suna zaune ne a Penmaen, dake kudanci kasar Wales ta masarautar Birtaniya. Kuma suna jiran kwamitin dake shirya kundin tarihi na duniya su zo su kwatanta karennasu da wasu karnuka guda biyu don a gwada aga wa yafi tsawo a tsakaninsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng