Tsagerun MEND sun nunawa Buratai yatsa
-Furucin Buratai ya harzuka tsagerun MEND
-Sun gargadi babban hafsan sojin Najeriya da ya iya bakinsa
-Sun yi kira ga jama’ar yankin da su yi hakuri da gwamnatin Buhari
Kungiya mai faufutukar kwato ‘yancin Niger Delta MEND, ta gargadi babban hafsan sojin Najeriya Janar Burutai da ya kame daga maganganu masu alaka da siyasa, da kuma son zuciya kan rikincin yankin.
A cewar jaridar Vanguard, kungiyar tsagerun MEND na mayar da maratani ne ga babban hafsan sojin kasar dangane da wani gargadi da ya yiwa tsagerun yankin masu gwagwarmaya da makamai da cewa, rundunar sojin kasar za ta yi amfani da karfin tuwo wajen murkushe su, idan suka gaza tattaunawa da gwamnatin tarraya kan kawo karshen barnar da suke yi a yankin.
A wata sanarwa da tsagerun MEND ta fitar a ranar Talata 26 ga watan Yuli, ta hannun kakakinta Jomo Gbomo, ta ce, kamata ya yi Burutai ya mayar da hankali kan ayyukansa na soji, ya kuma kaucewa maganganun da za su harzuka mutane. Sannan kungiyar tsagerun ta kara da cewa, “muna gargadi ga babban hafsan sojin da ya iya bakinsa tare da gujewa kalamai na siyasa da ka iya harzuka jama’a.”
Tsagerun MEND, a sanarwar ta yi kira ga jama’ar yankin da su yi hakuri da gwamnatin Buhari, ta kuma ce tare da taimakon wasu mutane, kungiyar na kokarin cimma wata matsaya da gwamnatin tarayya mai alfanu gare su.
Asali: Legit.ng