Dalilan da yasa wasu mazaje suke son zama da mata daya

 Dalilan da yasa wasu mazaje suke son zama da mata daya

Jami'in kula da Auratayyan ya bayyana cewar matan dake Aske gashin su, suna rage ma kansu daraja.

 Dalilan da yasa wasu mazaje suke son zama da mata daya

Acewar George Lutterodt, dan asalin kasar Ghana kuma jami'in kula da Auratayyan yace, duk macen da take Aske gashin kanta, to babu shakka tana rage ma kanta daraja ne, kuma zata fuskacin jarabawa na talauci.

Da yake magana da gidan Redio FM na Efisem show a Accra Kasapa, Lutterodt, ya jaddada cewar yanayin kwalliyar da mata sukeyima gashin su, bashike nufin suna kokarin nuna kwalliyar su bane. Yace yanayin gyaran nasu yana nuna damuwansu na cewar har izuwa lokacin basuda aure duk da tsawon shekarun su.

KU KARANTA : Gwamnati ta jajanta ma iyalan tsohon mataimamakin gwamnan kano

Ya kara da cewar, ku sani, Maza suna son mace ne sakamakon abunda suka gani a su, dakuma halayyar su. To ku kuma kun yanke gashin kanku, kunga kun ragema kanku shekaru, idan yan kananan yara sukace suna sonku, sai kuce Allah ya sauwaqe wannan abun kunya, Allah ya kyauta.

Shin kun yarda da maganar shi ko Baku yarda ba?

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng