Darajar Naira ta farfado a kasuwar bayan fage
Darajar takardar kudin Najeriya watau Naira ta farfado a kasuwannin bayan fage a yau inda aka tashi da sabon farashin da ake siyen $1 a kan N375 a maimakon N378 din da aka siyeta a jiya. Wannan dai yana nuni ne da cewar darajar Naira din ta karu da N3.
Wani maaikacin mu na jaridar Legit.ng shine ya bayyana mana haka. Ma'aikacin namu har ilayau ya kuma kara da cewa farfadowar darajar Naira din ba zai rasa nasaba ba da rade-raden da akeyi kan cewa babban bankin Najeriya watau Central Bank of Nigeria (CBN) zai fara saida kudaden dala din a kasuwannin kasar nan na canjin kudade.
Masu sana'ar canjin kudaden dai da suka zanta da ma'aikacin mu sun bayyana cewa dalilin da yasa darajar Naira din ta tabarbare tun farko mai rasa nasaba da sabon tsarin da babban bankin kasar nan CBN ya fito dashi watannin nan da suka gaba ta.
Wani dan canjin da mukayi fira da shi yace: "Ana rade-raden cewa babban bankin kasar nan watau CBN zai saida ma mu kudaden na dollar shi ne yasa wasu da suka boye tasu suka fitar a yau don suma su samu su siya indan an fara saidawa."
Mai karatu zai iya tunawa cewa a baya dai cikin watan Janairu babban bankin kasar nan ya hana yin cinikayyar kudaden bajen a kasuwannin bayan fage saboda a cewar sa babu isassun kudaden a wancen lokaci. Daga baya kuma sai babban bankin ya fito da wani tsarin yin canjin na daban da nufin kawo sauyi a kasuwar canjin da kuma farfado da darajar ta Naira. Ya zuwa yanzu dai hakan bata fara samuwa ba ganin yadda darajar kudin Naira din ta fadi har ya zuwa N375 a yanzu din.
Asali: Legit.ng