Kana cajin wayarka yadda ya kamata?

Kana cajin wayarka yadda ya kamata?

Kana yawan samun matsalan caji da batir din ka?  Cajin wayanka na kai maka zuwa yamma? Toh ga sauki yazo maka.

Kana cajin wayarka yadda ya kamata?

A wani bincike da masana ilimin kimiyya da fasaha suka yi, sun gano batir ma na gajiya, kamar yadda mutane ke gajiya, haka sinadaran cikin batir ke gajiya, idan kana son batirinka ya dade, toh ka dinga cajin wayanka yadda ya kamata. ga kadan daga cikin hanyoyin magance matsalar.

Kana cajin wayarka yadda ya kamata?

Cire waya daga caji idan ya cika

A daina barin waya a caji idan ya cika, haka babu kayau, muna yawan yin haka a cikin dare, da zaran waya ya cika dari bias dari, sai aka cigaba da caji, toh haka zai gajiyar da batir din wayanka.

 

Kada cajin ya kai kashi 100

Ba lallai sai ka caja batirin ka zuwa kashi 100 ba, bincike ya nuna haka, bai kamata ba. Saboda hakan na nufin kana sama batirinka wuta da yawa kenan, shima na kashe batir.

 

Caja waya a duk lokacin da ake so

Batir yafi dadewa idan ana cajinsa a lokutta kadan a rana, an fi so a caja waya idan ya sauka da kasha 10, sai dai an san yin hakan zai yi wuya, amma zaka iya cajin shi duk lokacin da ka samu dama. Caja batir kamar haka zai sa batirinka ya dade yayi karko, kuma zaka kasance da caji a kullum.

 

Ajiye waya wuri mai sanyi

Zafi na cutar da batirin waya sosai, idan hasken rana ya haska wayanka, toh ka tabbata ka kare fuskan wayar, don kiyaye karfin batirin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng