‘Yan majalisa sun caccaki Obasanjo kan furucinsa
-Tsohon shugaba Obasanji ya sha caccaka daga ‘yan majalisar bisa furucin da ya yi akan su
-Wasu na cewa Obasanjo dole ya nemi gafarar ‘yan majalisar
-Wasu kuma na cewa tsohon shugaban ba shi da bakin da zai zage su domin
Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo na fuskantar martani ne bisa kalaman da ya na cewa ‘yan majalisar taron barayi ne kuma ‘yan tasha, ga kadan daga cikin martanin na su;
Dan majalisa Agbonayima cewa ya yi, har yanzu ‘yan najeriya na bin Obasanjo bashin bayanin yadda ya yi da Dala miliyan 16 na gyaran wutar lantarki da suka bata a zamanin mulkinsa, amma kuma ya kiran wasu barayi, shugaban kwamitin kula da al’adu da kuma harkokin yawon shakatawa, Sanata Mathew Urhohide na PDP daga Edo, cewa ya ke yi, ya zama dole Obasanjo ya nemi gafarar ‘yan majalisar.
KU KARANTA: A rika sara ana duban bakin gatari –Sanata Ali Ndume
A nasa maratanin mataimakin shugaban marasa rinjaye Emanuel Bwacha cewa ya ke yi, Obasanjo ba shi da bakin da zai ce uffan game da cin hanci da rashawa domin shi har daburi ya ci, a lokacin shugabancinsa. Haka ma wani wakili Joan Aniocha mai wakiltar Oshimili a jihar Delta na cewa da ‘yan majalisar barayi ne, da sun karbi cin hanci da ya bayar, sun kuma gyara kundin tsarin mulki ya yi tazarce.
Bayan wata ganawa da ya yi da shugaba Buhari, Obasanjo ya bayyana ra’ayinsa ga manema labarai kan zargin aringizon kudade da ‘yan majalisar Wakiliai su ka yi wa kasafin kudi na 2016, a inda ya kira su da masu fashi da mukami, ya kuma ce hakan ya tabbatar da matsayinsa game da ‘yan majalisar na halayen gafiya tsira da na bakin ki ne.
Asali: Legit.ng