An kama Dan Najeriya kan Maganin  Kanjamau na karya

An kama Dan Najeriya kan Maganin Kanjamau na karya

-Dan Najeriyar An kama Shine Kan Sai Da Maganin Kanjamau Da Yakeyi Ga Wadanda Ba'a Tsammani.

Wani mutum mai suna Uzoma Eleazer an kamashi a kasar India da wasu mutane su 3 bayan yunkurin sai da maganin cutar kanjamau da suka yi ta yanar gizo na karya.  Kamar yadda muka samu rohoto Uzoma yayi yunkurin sai da wani magani wanda aka gano goro ne ga wani dan India wai shi Anil Mathur kimanin N10miliyanm.

Kamar yadda mathur ya bayyana ya hadu da Uzoma ta dandalin sadarwa suka kulla abota har Uzoma ya sa ya yadda da cewa yana da wani maganin na musamman da a kasar Najeriya kawai yake tsirowa,wanda yake da amfano da yawa har ya hada da maganin ciwon Kanjamau kuma Uzoman ya bayyana mai ana samun riba mai yawa a maganin na kanjamau. Uzoma ya sai da mai da giram 400 na maganin akan N400,000 a kawanne, wanda aake samu a Najeriya N4,400 a kowane kilo giram.

KU KARANTA : Sanata Shehu Sani ya bayyana akan auren jinsi ko auren dabbanci

An kama Uzoma da abokan sana'ar sa wanda aka bayyana sunayensu Taufiq Hussaain,Fatel Sayed da Yagesh Kumar Patil bayan yan sanda sun ga wayar tarho wanda yake amfani da ita gurin kiran Mathur da Na'ura mai kwakwalwa 3,da fakitin Goro da kudi har N1.9 miliyan. Mai magana da yawun yan sanda yace wadanda ake tuhumar duk suna hannu yan sanda har zuwa 27 juli,dan haka ana rokon duk wanda hakan ta taba faruwaa da shi ya kawo ma yan sanda rohoto.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel