Tsohon mataimakin gwamnan Kano ya rasu

Tsohon mataimakin gwamnan Kano ya rasu

An tashi da alhini da jimami a ranar lahadin data gabata a jihar Kano biyo bayan rasuwar sanannen dan siyasan nan kuma tsohon mataimakin gwamnan jihar Engineer Magaji Abdullahi.

Tsohon mataimakin gwamnan Kano ya rasu
Marigayi Magaji Abdullahi

Kamar yadda wani hadiminsa ya fadi, Abdullahi kwakwatawa, Magaji Abdullahi ya rasu yana da shekaru 69 bayan wata gajeruwar rashin lafiya a Asibiti.

Tsohon mataimakin gwamnan Kano ya rasu
Jana'izar sa

Tsohon shahararren dan siyasan ya taba kasancewa mataimakin gwamna ga Malam Ibrahim Shekarau daga 2003-2007.

Asali: Legit.ng

Online view pixel