Jihar Sakkwato na yunkurin amfana da kudin kasar Kuwait
– Gwamnatin Jihar Sakkwato tace tana iyakan kokarinta wajen ganin cewa ta amfana da kasar Kuwait ta sadaukar domin cigaban kasashen Afrika ta yamma kudi $1 bilyan
– Tambuwal da gwamnatin Jihar na kuma yunkurin hadaka wajen gudanar da ibadan Zakkah
Daga cikin yunkurin karfafa hadaka ta bangaren Ilimi, Al'adu,da Kasuwanci da kasar Kuwait, gwamnatin Jihar Sakkwato tace tana yunkurin amfana daga kudin kasar Kuwait. Kudin da ta sadaukar ma kasashen Afirka ta yamma domin kawo cigaba a bangarorin kasashen masu muhimmanci.
Yayinda ya kai ziyara ofishin jakadan kasar Kuwait da ke Abuja, Gwamna Aminu Waziri Tambuwal yace tunda gwamnatin kasar Kuwait ta sadaukar da kudin a shekaran 2013,wanda za'ayi amfani dasu cikin shekaru 5, an aiwatar da ayyuka da dama a nahiyar Afrika
“ Muna mika kokon baranmu gareku saboda samun amfana daga kudin domin inganta bangarora kaman koshin lafiya,ilimi,samar da ruwan sha,da cigaban mata. Muna sane da cewa wasu kasashen Afrika sun amfana daga akasarin kudin,amma muna yunkurin cewa mu ma mun amfana da shi ko yaya ne. Kana, muna kyautata zaton zamu iya fadada alaka da kasar Kuwait kuma na zo ne domin gayyatar su domin su zuba jari a bangarora masu riba kaman aikin noma,da hakan ma'adinai a Jihar Sakkwato.” Tambuwal ya fada.
KU KARANTA : Mun ba Buhari makonni 3 – ‘Yan bindiga
Gwamnan ya kara da cewa kasar Kuwait da jihar Sakkwato na kara hadaka wajen gudanar da ibadan zakkah da sadaka.
A Jawabin jakadan kasar Kuwait , Dr. Abdulaziz Ahmad Al-Sharrah, ya yabawa gwamnatin jihar Sakkwato da nuna aniyarta na bukatan amfana da kudin ,ya ce kasar sa na shirye da ta karfafa hadaka da Najeriya da wasu kasashen Afrika. Wasu bangarorin hada kan za suka tattauna shine al'adu, cigaban ma'aikatu,cigaban tattalin arziki tsakanin bangarorin 2.
Asali: Legit.ng