Civilian JTF 250 sun shiga aikin Soja
Jimillan tsaffin masu farar hulan da taimakawa soji wajan yaki da Boko Haram watau Civilian JTF guda 250 sun karashe wa’adin horon Soja kuma sun shiga aikin Soja yanzu.
Gwamnan Jihar Barno Kashim Shettima ya sanar da hakan a ranar juma’a ,22 ga watan yuli a Maiduguri,babban Birnin Jihar Barno.
Shugaban tawagar, Benjamin Solomon ,yayinda yake Magana da a madadin duka sabbin kuratan, yace “ Muna nan muna godiya da muka sojojin kasar mu. Muna mika godiyan mu ga shugaban kasa, da baban mu shugaban hafsoshin Sojin Najeriya, wanda ya tabbatar da cewa mun zama sojoji a yau. Muna da yawa a jihar kuma muna rokon cewa wasunmu su samu damar da muka samu a yau na zama Soja.”
Muna da masu digiri a cikin mu wadanda zasu iya samun daman zama hafsoshin sojin kasa. Amma ga mu, lokaci yayi da zamu yi ma kasan mu bauta, mun mika rayuwar mu domin kare bangarorin Najeriya.
KU KARANTA : An kubuto ‘yan mata da yara daga wajen ‘Yan Boko Haram
Sabbin Sojojin da suka kasance masu taimaka wa sojoji wajen yaki da boko haram yanzu zasu zama ma’aikatn Jihar Barno. Wasu mambonin civilian JTF zasu shiga aikin yan sanda, aikin DSS da wasu jami’an tsaro. Ku tuna cewa civilian JTF sun tabbatar da zaman lafiya da tsaro a garuruwan da boko harm suka kwace, musamman jihohin Barno,Yobe, Adamawa, da kuma wuraren da yan sanda da sojoji suka gaza.
Asali: Legit.ng