Barcelona ta sayi shahararren dan wasa

Barcelona ta sayi shahararren dan wasa

Kungiyar kwallon kafa dake kasar Sifen wato Barcelona ta tabbatar da yarjejeniyar da ta shiga da kungiyar Valencin na siyan dan wasan ta na tsakiya Andre Gomes dan kasar Portugal.

Barcelona ta sayi shahararren dan wasa
Andre Gomes

Gomes ya shafe shekaru biyu a Valencia tun sa’adda ya tafi kulob din daga Benfica a shekarar 2014. Akwai jitajitan cewa Barcelona ta biya euro miliyan 40 don siyan dan wasan wanda ya buga Valencia wasanni 30 kuma yaci kwallaye 3 a kakar wasa ta bara.

Gomes dan shekaru 22 ya buga ma kasar Portugal wasanni 13, kuma yana daga cikin yan wasan da suka fafata a wasan karshe na gasar cin kofin nahiyar turai da kasar Portugal ta lashe. Akwai alamun Real Madrid ma ta nemi zawarcin sa, idan cinikin da wasan ta kaya, Gomes zai kasance sabon dan wasa da Barcelona ta siya a kwana kwanan nan tun bayan data siya Samuel Umtiti, Lucas Digne da kuma Denis Suarez.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng