Liverpool sun kammala siyayyar su ta 6

Liverpool sun kammala siyayyar su ta 6

Wata kafar labarai ta kungiyar Liverpool sun sanar da cewa dan kasar Netherlands din nan wanda kuma yake buga wasa a kungiyar Newcastle watau Georgino Wijnaldum zai koma kungiyar bayan an kammala masa gwaje-gwajen lafiyar sa.

Liverpool sun kammala siyayyar su ta 6

Kafar ta labarai ta kuma ce dan wasan zai bi sauran tawagar sa ta Liverpool a can kasar Amuruka da zarar an kammala gwaje-gwajen. An dai kiyasta dan wasan zai koma Liverpool din ne a kan kudi £23m. Shi dai dan wasan ya zura kwallaye 11 a gasar firimiyar da ta gabata a tsohon kulob din sa kafin daga bisani su fada gurbin gajiyayyu.

Indai har ta tabbata to hakan zai maida shi cikon siyayya ta 6 da Liverpool din tayi kuma na biyu wajen tsada bayan Sadio Mane wanda aka sayo £30m daga Southampton. Kungiyar ta Liverpool dai tuni ta kammala siyen Mane, Joel Matip, Marko Grujic, Loris Karius da kuma Ragnar Klavan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel