Dortmund ta kammala siyen dan wasan Bayern Munich
Kungiyar wasan kwallon kafa dake kasar Gamani watau Borussia Dortmund ta tabbatar da kammala siyen dan wasan nan na Bayern Munich Mario Gotze.
Shidai dan wasan daman ya bar Dortmund din ne a shekarun baya yayin kuma da yanzu ya dawo kungiyar tasa ta da. Shi dai Mario Gotze ya bar kungiyar Dortmund ne a shekarar 2013 bayan da ya zura kwallaye 31 cikin wasanni 116 tun bayan da ya soma buga kwallo cikin shekara 2008.
Lokacin da yake tsokaci game da komawar tasa, dan wasan mai shekaru 24 ya ce: "Lokacin da na bar Dortmund zuwa Bayern, nayi hakan ne ina sani. Bazan yi wani boye-boye ba." Haka ma Gotze ya cigaba da cewa: "shekaru 3 kenan bayan faruwar hakan sai na sake duba tunanin da nayi na kuma yanke shawarar in dawo duk kuwa da cewa magoya bayan Dortmund din da yawa ba zasu fahim ci hakan ba."
Ya kara da cewa: "I dan na fara bugawa, ina so ne in gamsar da kowa. Ina so in taimaka ma kungiyar tawa. Ina so in farantwa magoya bayan mu rai." Shi dai dan wasan ya buga wasanni 14 ne kacan a kakar wasannin da ta gabata a kulob din na Bayern.
Asali: Legit.ng