Ra’ayi: Dalilin da yasa yayan Buhari suka yi karatu a kasan waje

Ra’ayi: Dalilin da yasa yayan Buhari suka yi karatu a kasan waje

wani masani akan harkan watsa labarai Femi Owolabi, yayi tsokaci akan labarin daya yawaita na yayan Shugaba Buhari da suka kammala karatu a kasar Ingila.

Ra’ayi: Dalilin da yasa yayan Buhari suka yi karatu a kasan waje
Shugaba Buhari da yarsa Zahra

Marubucin ya bayyana rashin jindadinsa ta yadda shugaban kasa yayi watsi da sha’anin ilimi a kasar nan a shafinsa na facebook.

A jiya ne tsohon mai magana da yawun tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan Reuben Abati ya taya yarsa murna a shafin twitter da ta kammala karatun ta daga Jami’ar Bristol dake kasar Ingila. Abin da yan siyasan mu suke nuna mana shine yayansu sunfi karfin makarantun gwamnati.

Ra’ayi: Dalilin da yasa yayan Buhari suka yi karatu a kasan waje
Reuben Abati da yarsa

Suna da gaskiya, saboda banga yadda za’ayi ace wai Yusuf Buhari yaje yana bin layin shiga mota da tsakar rana da zata dauke shi daga Bosso zuwa Gidan kwano reshen jami’ar kimiyya da fasaha dake garin minna ba.

Sa’annan bazan iya misalta cewa wai ga Zahra Buhari cakude da su Dare Zainab Oniyangi, Safiya Mohammad, Kafayat Saleeman da sauran dalibai da yawan su ya kai 1000 ba makure a cikin dakin karatu dake Bosso wanda an gina shi don daukan dalibai 250 ne. zai yi wuya ace Elizabeth Abati ta iya jira na tsawon awanni a dakin gwaje gwaje na kimiyya duk don tana jiran a kawo wuta tayi nata gwaje gajen.

Ra’ayi: Dalilin da yasa yayan Buhari suka yi karatu a kasan waje
Yusuf Buhari

Ko kuwa akwai daya daga cikinsu da zai iya zama tare da Wale Ajayi a D-Block suyi ta karatu har wayewar gari da kyandir. Ana yi shugaban kasa sunan shine bakon duk jami’o’in gwamnatin tarayya, a don haka kar shuwagabannin siyasa ke kallonsa na kin sanya yayansa a makarantu da gamnatin sa ke kula dasu. Wannan tsarin karatun ya lalace, sa’annan yan siyasa wandanda sune ummul haba’isun lalacewar tsarin sun dauke yayansu zuwa makarantu a kasar Ingila.

Wannan Ra’ayin Wale Ajayi ne marubucin kasidar, don haka bai zama lallai ya kasance ra’ayin Legit.ng ba. Muna maraba da naku kasidun a info@naij.com. Ka turo mana da sakon karta kwana dangane da abin da kake son yin rubutu akai da kuma dalilin ka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel