Jarimar yar wasan Najeriyan FIM Lola Alao ta canza addini

Jarimar yar wasan Najeriyan FIM Lola Alao ta canza addini

- Jarimar yan wasan Nageriya fim Lola Alao ta canza addini zuwa addinin musulunci.

- Har ila yau kuma jarimar ta canza sunan ta.

- Tabi sahun su Lizzy Anajorin, Fathia Balogun da sauran su.

Jarimar yan wasan Nageriya fim Lola Alao ta canza addinin ta na kiristanci zuwa musulunci. Jarimar dai ta canza addinin nata ne a ranar Talata 19 ga watan yuli a Acadamic of propagation, najeriya wanda akafi sani da [ACADIP].

Jarimar yar wasan Najeriyan FIM Lola Alao ta canza addini

Jarimar har ila yau ta canza sunan ta zuwa Rhodiyat. Shugaban kungiyar Adepoju Yusuf shiya yada labarin, ya kara da cewa, godiya ya tabbata ga Allah; ku tayani yima Lola Alao [jarimar yar wasan Najeriya fim] murna, saboda ayau ta amshi kalmar shahada daga wajena. Kuma ta zabi Rhodiyat a matsayin sabon sunan ta. Allah ya yarda da ita amatsayin musulma, kuma yasa mata albarka akan duk wani abunda zatayi a rayuwanta, amin.

Alao dai ba itace ta farko a cikin yan wasan Najeriyan fim data fara musulunta ba, akwai jarima mai suna Lizzy Anjorin wanda ake ce mata Elizabeth Anjorin ada, ita ta fara musulinta harma taje aikin Hajji.

KU KARANTA : Me musulunci yace game da zaman aure da ‘ya mace?

Har ila yau, jarima mai suna Fathia Balogun an bata suna na musamman wato Atesinse Adinni. Kamar Alao, Fathia ada kirista ce kafin ta musulunta taje aikin hajji.

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel