Wani dan bautar kasa ya shiga tsomomuwa bayan ya kwanta da matar wani
An maka wani matashi mai yima kasa hidima watau National Youth Service Corps (NYSC) kotu a garin Abuja bisa zarginsa da akeyi da kwantawa da wata matar aure.
Wata jarida mai suna Eagle Online ce dai ta ruwaito cewa mijin wata mai suna Mr. Anozie shine ya maka matashin kotu a bisa zargin sa da kwantawa da matarsa ba ma sau daya ba a ranar 24 ga watan Maris din da ya gabata. Mr. Anozie ya kara da cewa yana karar matashin ne bisa ga zargin kwantawa da yake yi da matarsa duk kuwa da cewa yasan tana da aure tun 18 ga watan Disemba na 2014.
Magidancin ya shaidawa kotun cewa ya taba kiran matashin mai suna Bonaventure a wayar sa inda ya tabbatar masa da cewa ya kwanta da matar tasa. Haka zalika Mr Anoza yace: "tun a lokacin nayi masa kashedin cewa ya rabu da ita don matata ce amma sai yayi kunnen uwar-shege da kashedin nawa."
Mr Anoza ya cigaba da cewa: "akwai ma wani lokaci da matashin ya aika wa matar tawa da kudin mota taje wurin sa daga makarantar ta a garin Anambra inda ta zauna tare dashi na wani tsawon lokaci. Daga karshe sai mai karar ya bukaci kotun data hukunta matashin don kuma yayi fasikanci da matar tasa sau da yawa.
To fa! Wata sabuwa wai inji 'yan caca.
Asali: Legit.ng