Motar da tafi tsada a Duniya tayi hatsari a Jamani

Motar da tafi tsada a Duniya tayi hatsari a Jamani

Wata mota mai matsananciyar gudu mai suna Koenigsegg da kudinta ya kai dala miliyan 6, kimanin naira biliyan 2 kenan tayi hatsari a lokacin da ake gwajin ta a filin gwajin mota na garin Nurburgrung dake Jamani, hakan yasa ta kasance daya daga cikin hatsari mafi muni da tsada da wata mota ta taba yi a tarihin mota.

Motar da tafi tsada a Duniya tayi hatsari a Jamani
Motar a yayin gwajinta

An samu labarin motar ta kufce ma direbanta ne inda yayi sanadiyyar kutsawa da tayi cikin shingen kariya dake gefen hanyar har ta wuntsula cikin rami. Motar 6a kufce ma direban ne a daidai wata kwanar mutuwa inda daga nan kawai sai tayi cikin shingayen.

Motar da tafi tsada a Duniya tayi hatsari a Jamani
motar bayan tayi hatsari

Daya ne kadai daga cikin ire iren motocin guda bakwai da aka taba kerasu ta taba samun matsala a sashin gabanta, da kuma gobara. shima wannan hadarin na ban mamaki ya faru ne a ranar litinin 18 ga watan yulio.

 

Labarai ya ishe mu cewa an wuce da direban motar zuwa Asibiti don a duba lafiyar shi, inda daga bisani kuma aka sallameshi, kuma kamfanin Koenigsegg ta tabbatar da haka.

Motar da tafi tsada a Duniya tayi hatsari a Jamani
Motar da tafi tsada a Duniya tayi hatsari a Jamani

Kamfanin Koenigsegg ta fitar da wata sanarwa dangane da hatsarin, inda take cewa “motar Koenigsegg motace mai matukar aiki, don haka dole ne a gwada ta yadda ya kamata.

 

“Motar na dauke da engine mai cin lita 5 biyar na mai, wanda ke sata gudun wuce sa’a, hakan na da hatsari matuka, don haka ya kamata a tafiyar da gwajin kadan kadan cikin dabara, mafi muhimmancin bukatar mu shine kare lafiyar matuka mota, don haka duk wani gwajin da mukeyi na kan ka’ida.”

Motar da tafi tsada a Duniya tayi hatsari a Jamani

ta kara da cewa “Alamun shaidar tayar motan da aka gani akan titin ya nuna irin faman da direban motar yayi da ita kafin ya afka ma shingen. Wannan karin manuniya ce ga yadda tuki ked a wahala akan hanyoyin cikin wannan filin tuka motan .

 

“A gaskiya bamu ji dadin wannan lamarin ba, amma munyi murnan ganin cewa tsarin tsaron da muka sa a motar ya taimaka wajen tserar da direban.” A yanzu haka kamfanin Koenigsegg na tallata motar akan kusan dala miliyan 6, kwatankwacin naira biliyan 2, Motar na dauke da engine mai cin lita 5 biyar na mai, wanda ke sata gudun wuce sa’a.”

 

Motar na gudun kilomita 400 cikin sakan 20, kuma birkin ta na kamawa a sakan 10.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng