Wani uba ya yiwa ‘yar sa ciki a Lagos
Rundunar ‘yan sanda ta jihar Legas ta kama wani mutum dan shekara 36, da zargin laifin yi wa ‘yar sa mai shekara 16 ciki da kuma kokarin zubar da shi.
Wanda ake zargi Kenney Micheal ya shiga hannun ‘yan sanda ne bayan da wata makwabciyarsa mai suna Uche wacce ya nemi ya lalata mata ‘yarta mai watanni 18 ta tona masa asiri Asirin uba Micheal ya tonu ne a lokacin da ‘yarsa Maria ta kamu da rashin lafiya, aka kuma kai ta asibiti a inda aka gano tana da juna biyu, a cewar Uche, “budurwar Michel, Ijeoma ta taimakawa masa da zubar cikin.”
Bayan ya shiga hannu, Micheal ya masa cewa yana kwanciya da ‘yar sa Maria tun cikin shekarar 2014 a lokacin tana ‘yar shekara 14 tun bayar da suka rabu da mahaifiyar ‘yar, shi kuma ya taho da ‘yar zuwa Legas.
A cewar Mari, kwanciya ta baya-bayan nan da babanta Micheal yayi da ita, ita ce ta ranar 8 ga watan Yuli. An kuma damke Micheal a ranar Talata 12 ga watan Yuli bayan da wata kungiya mai kare hakkin yara da hana cin zarafin mata ta jihar ta shige gaba kan maganar.
Makwabciyar Micheal, Uche wacce ta tona asirinsu ta ce a baya, Micheal din ya yi kokarin lalata ‘yar ta mai watanni 18 ta hanyar sa mata a gabanta, ta kuma kai karar sa ofishin ‘yan sanda amma aka kashe maganar, ta kuma ce ta na jin labarin abin da Micheal ya yiwa ‘yar sa a bakin kawayenta, sai ta sake garzaya wurin ‘yan sanda, wanda ya sa aka damke shi da buduwarsa.
Asali: Legit.ng