Klopp ya bayyana yan wasa 6 da za su bar Liverpool

Klopp ya bayyana yan wasa 6 da za su bar Liverpool

Mai horarwar kungiyar Liverpool Jurgen Klopp ya bayyana wadansu yan wasa su 6 tare da tsoratar da su da cewa idan dai har basu tashi ba to kam ba zasu buga wasa karkashin sa ba a kakar wasa mai zuwa.

Klopp ya bayyana yan wasa 6 da za su bar Liverpool
Jurgen Klopp

Klopp din ya bayyana cewa tunda kungiyar Liverpool ba zata buga wasannin kin kofin turai ba wannan yana nuni da cewa wasanni yan kadan ne kungiyar zata buga a kakar wasa mai zuwa wanda hakan ne kuma ba zai bada dama ba ga reshi da ya sa yan wasan su buga.

Jaridar Mirror ta kasar Ingila dai ta ruwaito cewa Klopp din ya shawarci Christian Benteke, Lucas, Adam Bogdan, Tiago Ilori, Mario Balotelli da ma Lazar Markovic da su bar kungiyar kawai. Tuni dai daman Jordan ibe da Martin Skrtel suka bar kungiyar a kakar cinikayyar nan zuwa Bournemouth da Fanerbache.

An ruwaito Klopp din dai yana cewa: "zamu samu wasu yan chanje-chanje nan zuwa can. Tabbas babu wani anfani dan wasa ya zauna kungiya koda kuwa ba zai samu damar buga kwallon ba. Idan baka da damar bugawa ai banga dalilin zaman mutum ba. Ba wani anfani."

"Nasan akwai wadansu yan wasan dake son su tashi kuma ina kyautata zaton hakan zai faru. Ina sa ran kuma wasu yan kwallon 2 zuwa 3 zasu zo suma kafin rufe kasuwar cinikayyar."Tun bayan bude kasuwar cinikayyar dai, kungiyar ta Liverpool ta siyi adio Mane, Joel Matip, Loris Karius da kuma Marko Grujic.

Asali: Legit.ng

Online view pixel