Tarihi: Sarkin Musulmi na farko a Lagos 1895

Tarihi: Sarkin Musulmi na farko a Lagos 1895

 A wannan shiri na waiwaye, Legit.ng ta yi waiwayi tarihin Sarki William Abass, shugaban ul’ummar Musulmi na farko a tarihin kafuwar Legas.

Tarihi: Sarkin Musulmi na farko a Lagos 1895
Sarkin Badagry na farko kuma shugaban Al'ummar Musulmi a Legas a zamanin turawa

Tarihi ya nuna cewa na haifi Sarki William Abbas ne a wani wuri da ake kira Ijoga Orile ta jihar Ogun a inda aka rada masa suna Famerilekun.

Yana dan shekara 6 wasu mahara daga kasar Dahomey suka kame shi, suka kuma sayar da shi ga wani malamin Islama kuma mai cinikin bayi da ake kira Sarki Abbas, bisa al’adara waccan lokaci bayi na amfani ne da sunayen iyayen gidansu, don haka sai ya rika sunan amsa sunan ubangidansa Abass.

An sake sayar da Abass ga wani mai cinikin bayi daga Barazil a mai suna Williams wanda ya tafi da shi can kasar, ya kuma rike shi a matsayin baran gidansa a maimakon ya sayar da shi. Da haka ya soma amsa sunan Willams, yayin da ubangidansa ya koya masa karatu da rubutu, A cewar wani mai kula da dakin adana kayan tarihin nan Badagry, Anago Osho.

Ganin hazaka da baiwar da Allah ya ba Seriki Abbas na iya harsunan Portuguesse da Ingilishi da Dutch, da kuma Spaniyanci, sai ubangidansa ya ‘yanta shi da kuma mayar da shi abokin harkarsa ta sayen bayi, sanna ya kuma dauki nauyin dawowarsa gida Africa, a inda ya zauna a Ofin , Daga baya ya koma Badagry a 1830, a shekarar 1895 Serika ya zama hamshakin attajirin da aka nada shi sarkin alummar muslmin daukacin kasar yarbawa har da Ebado.

Daga baya Major J.E Ewart ya ba shi sarautar Badagry a 1895, Abbas ya kuma gina babban masallacin juma’a na Badagry a Sango. Sannan ya rasu a 1919, ya kuma auri mata 128, ya kuma haifi ‘ya ‘ya 144,  ya kuma bar zuriya mai yawa wadanda aka ce sun watsu a Najeriya har a jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel