N'Golo Kante ya bada dalilin shiga Chelsea
1 - tsawon mintuna
– N’Golo Kante yace Antonio Conte ya jawo shi shiga Chelsea
-Bafaranshen yana gode ma magoya baya da karamta shi
-Kante shine na biyu da shiga Blues bayan Michy Batshuayi
An dai sayi dan wasan mai shekara 25 daga wajen zakkarun kwallo na Leicester a kan kudi £32miliyan, abin da ba'a taba ganin irinsa ba.
Ya ci gaba da cewa "gawurtaccen klub ne, wanda ya dauki gawurtaccen koci, yana kuma da kishin ci gaba irin wanda na ke so. Abin da klub din ya sa gaba, da maganar da kocin yayi suka sa nace da ni za'a yi wannan gagarumar abu mai dadi".
KU KARANTA : Kocin Chelsea Antonio Conte ya yaba ma N’golo Kante
Asali: Legit.ng