Gwamnoni biyar da Shugaba Buhari yafi kauna

Gwamnoni biyar da Shugaba Buhari yafi kauna

Kamar kowani dan adam, Shugaba Buhari shima yana da irin nasa muradun, gwamnoni biyar ne daga cikin 36 suka fi soyuwa a wurin Shugaban kasa Buhari.

Zai iya tattauna dalilan da suka sa Buhari yafi kaunar su, amma ba laifi bane ace dan adam ya fi son wani mutum sama da wani. Sa dai akwai wasu dalilai da ka iya sad an Adam yaji yafi son yin aiki tare da wani sama da wanin sa, duk da haka, wasu dalilan ba za’a iya fayyace su ba.

 

1- Ibikunle Amosun-Gwaman Ogun

Al’ummar jihar Ogun sunfi sanin Gwamna Amosun da taken ‘SIA’, wanda ke nufin Sanata Ibukunle Amosun.

Gwamnoni biyar da Shugaba Buhari yafi kauna

Amosun tsohon da majalisa ya kasance daya daga cikin masu matukar kaunar Shugaba Muhammadu Buhari a lokacin da suke cikin jam’iyar ANPP a farkon shekara ta dubu biyu-2000, dukkanin su sunyi takara a cikin Jam’iyar na gwamna da na shugaban kasa inda suka sha kaye a hannun jam’iyar PDP.

Kadan daga cikin irin soyayyar da shugaba Buhari ya nuna ma Amosun kauna shine; ya ziyarci jihar Ogun a watanni kadan da suka gabata. Ba wai kawai Buhari ya ziyarci jihar bane, a’a, sai da ya kwashe akalla kwanaki biyu a can, inda kuma ya kaddamar da ayyuka da dama.

Amosun wanda yake tsohon akanta ne ya shiga gaban sauran gwamnoni biyar ta hanyar sanya wa wani rukunin gidaje da ake gan ginawa suna Muhammadu Buhari Estate wato rukunin gidajen Muhammadu Buhari. Kazalika kuma, bayan fasa da shugaba Buhari yayi na kai ziyara jihar Legas a kwanakin baya, sai gashi washegari an ganshi yana tarban gwamna Amosun.

A iya tunawa harda Amosun a cikin tawagar da tar aka Shugaba Buhari zuwa garin Makkah domin yin umarah, sa’annan ya raka Shugaba Buhari tattakin da yayi zuwa kasar Sin na tsawon kwanaki 7, bugu da kari gwamna Amosun na daga cikin gwamnoni kalilan da shugaba Buhari ya zagaya dasu cikin gonar su dake Daura.

 

2- Aminu Bello Masari-Gwamnan Katsina

Gwamna Masari ya kasance tsohon kakakin majalisar wakilai ta kasa. Gwamnan ya tsaya tsayin daka tare da shugaba Buhari a shekara 2011 lokacin da suka sha mummunar kayi a zabukan shekarar. Dukkaninsu sunyi takara a karkashin jam’iyar CPC na gwamna da na shugaban kasa a 2011.

Gwamnoni biyar da Shugaba Buhari yafi kauna

Shugaba Buhari na son Masari saboda saukin kansa, shugaban kasa ba yi wata wata ba wajen yanke shawarar mara wa Masari baya don tsayawa takarar gwamnan jihar Katsina a shekarar 2011 a karkashin jam’iyar APC.

Ganin cewa shugaba Buhari dan asalin jihar Katsina ne, toh ba zai yi wasa da mutumin da ke jagorantar adawa a jihar ba, balle ma idan suna da akisa iri daya kuma suna jam’iya daya.

 

3- Kashim Shettima-Gwamnan Borno

Ana yi gwamna Kashim Shettima kirari da ‘mage mai rayuka tara’ saboda irin kwaramniyar da ya dinga shad a yan ta’addan Bokohara har na kusan shekaru 5. Wannan jarumta tashi abin a yaba ne.

Gwamnoni biyar da Shugaba Buhari yafi kauna

A yayin yawonn neman kuri’u da APC ta gudanar a bara,Buhari ya bayyana cewa Borno na daya daga cikin manyan muradunsa, haka ko aka yi, Shugaba Buhari ya cika musu alkawarinsa inda ya tura sojoji su yaki yan Bokoharam.

Shugaba Buhari ya ziyarci jihar Borno sau dayawa, kuma ta baiwa gwamnan tabbacin zai taimakeshi wajen dawo da martabar jihar. Dangane da maganan albashi kuwa, a baya bayan nan ne gwamnan ya ce babu wani ma’aikaci dake binsa bashi, wannan ma abin a yaba ne.

 

4- Abdulaziz Yari- Gwmnan Zamfara

Gwamna Yari shine shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya. Za’a iya cewa gwamnan Zamfaran yana daga cikin mutanen da Buhari ke ji dasu a fiye da sauran gwamnonin Arewa. Buhari ya yarda da gwamna Yari matuka, wanda hakan yasa ya zabi jiharsa cikin jihohi kalilan da yi ziyara a cikin watan yulio.

Gwamnoni biyar da Shugaba Buhari yafi kauna

Ba wai kawai shugaban yaje yawon shakatawa bane jihar Zamfara, a’a, har said a ya kaddamar da wasu manya manyan ayyukan hanyoyi. Kada ya ba yan Najeriya mamaki idan shugaba Buhari ya mara masa baya don ya gaji kujerarsa ta shugaban kasa a 2019 idan dai har ba zai tsaya takara ba.

 

5- Abiola Ajimobi-Gwamnan Oyo

Ma’aikata na matukar fushi da gwamna Ajimobi biyi bayan watsi da yayi da al’amuran biyan albashin su. Gwamnan ya shiga rikici da kungiyar kwadago rashen jihar wanda hakan yayi sanadiyyar kai karar kungiyar kwadago kotu da yayi.

Gwamnoni biyar da Shugaba Buhari yafi kauna

Sai dai a wani hannun kuma, gwamnan na daga cikin mutanen da shugaba Buhari ke ji dasu, dalili kuwa shine, gwamnan na da alaka mai kyau da shugaba Buhari tun zamanin da suke jam’iyar ANPP, sun ci sun sha tare, wanda hakan yasa shugaban ba zai manta das hi ba.

 

Sanata Ajimobi ya kasance cikin tawagogin da suka raka shugaba Buhari yawancin kasashen da ya ziyarta, haka kuma shugaba Buhari ya wakilta shi da ya rattafa hannu akan wasu takardu a madadin Najeriya a yayin ziyaransu kasar Sin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng