An kama wani limamin cocin katolika da neman yin lalata

An kama wani limamin cocin katolika da neman yin lalata

- An dai kama shi limamin katolikan ne a ayayin da yake kokarin biyan kudi domin yayi lalata da wata.                          

- Limamin dai ya shiga hannu ne alokacin da yake yunkurin biyan wasu kudi domin yayi lalata da wata mace.

A kwanakin bayane dai aka kama limamin da nufin biyan kudi domin yayi lalata a USA, shi dan shekara 40 din da haihuwa mai suna Dominic Yomoah baisan cewar da ma'aikaciyar hukumar yan Sanda na farin Kaya yake magana ba alokacin da yake kokarin yi mata tayin kudi domin ya samu hadin kai nayin lalata da ita.

An kama wani limamin cocin katolika da neman yin lalata

Abun dai ya farune ranar asabar 9 ga Watan yuli. Yamoah wanda shine limamin saint Clara parish wanda ke clarinda dakuma st.Joseph parish wanda ke Vivisca, an kamashi kuma an kaishi fremont country law enforcement center dake California a USA.

Acewar shashin yada labarai na hukumar yan sandan, bincike ya nuna cewar ya dauka da karuwa yake magana a hamburg wanda hakan ya janyo aka kamashi a ranar asabar da safe. Wanda shi wanda ake zargi da aikata wannan abun wato Rev. Dominic Yomoah a county yake da zama, dan shekaru 40 da haihuwan dai yayi kokarin ta bashi hadin kai domin yayi lalata da ita akan kudi $2,000, inda baisan cewar da jami'an tsaro na farin Kaya yake magana ba.

KU KARANTA : Tirkashi : Fasto mai auren jinsi ya fito yayi magana

Shashin lower state patrol suka taimaka wajan binciken gaskiyar abunda ya faru. Majiyar tadai rawaito cewar, hukumomin Roman Catholic sun dakatar dashi daga gudanar da duk wani abu a cochin. Abun mamaki.

 

 

 

 

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng