Majalisar dattijai ta mayar da martani ga APC

Majalisar dattijai ta mayar da martani ga APC

Majalisar Dattijai ta mayar da martani ga APC, inda take bata shawara da ta daina fadin zantuttukan da zasu rika rura wutan siyaysan Najeriya, majalisar ta baiwa Jam’iyar shawaran ta rika tabbatar da sahihancin labari balle ma akan irin wanda take maganan wai za’a tsige Buhari kafin ta fara maganganu. Majalisar ta caccaki Jam’iyar da akan yada labaran kanzon kurege na tsige shugaba Buhari,

Majalisar dattijai ta mayar da martani ga APC
Majalisa

Majalisar tace tayi matukar mamakin cewa duk da rinjayen da jam’iya take dashi a majalisar, amma jam’iyar ta kasa tabbatar da wannan batu daga yayanta wadanda suk halarci zaman tattunawan kafin ta yi tsokaci.

 

Jam’iar APC dai ta yi watsi da maganan tsige Shugaba Buhari, inda ta danganta shi da abin dariya, jaridar Daily Post ta ruwaito sanata Aliyu Sahabi mai magan da yawun majalisar dattijai a wata sanarwa da ya fitar a ranar alhamis 14 ga watan yulio yana cewa “mun yi tsammanin jam’iyar zata dan yi kokarin duba zancen ta fuskoki da dama don tantance sahihancin sa wanda tun a fari ma karya ne irin na wadanda suka rubuta labarin da masu daukan nauyinsu”

 

“ya kamata shugabancin APC su gane cewa da akwai kamshin gaskiya a lamarin, toh da an jingina zancen ga wani sanata wanda ya halarci zaman da aka yi. “a fayyace take cewa a zaman da mukayi a ranar laraba majalisar kanta ta dimautu da irin wannan karyan, wanda haka cin keta rigar mutuncin yayan majalisar ne, dalilin da yasa kenan muka umarci kwamitin da’a da amsan koke koke da ya binciko mana majiyar wannan zancen, da har ya kai ga yin wannan karya.

 

Daga kasrhe ya shawarci APC da ta rika tantance gaskiya a koyaushe kuma akan dukkan lamarin da ya shafi majalisun kasar nan kafin ta dauki wani matsayi, yayi nuni ga rashin yin hakan zai ruruta wautan siyasan kasar nan. ya kara da cewa “muna so mu tabbatar ma jam’iyar cewa majalisar dattijai na girmama dimukrodiyam dake gudana a kasarnan, kuma ba zamu taba kasance wa masu mata zagon kasa ba."

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng