Sojojin Ruwa Sun Kama Wani Mutum Mai Damfarar Masu Neman Aiki
-Ma'aikatan sojin ruwa da aka tura Calabar,Babban birnin jahar Cross River sun cafke wani wai Mr. Pius wanda ke damafarar mutane a matsayin sojan ruwa.
Daraktan sadarwa na sojojin ruwa na Kasa Commorode Christ Ezekobe ya bayyana yadda wanda aka kama yake damfarar masu neman aiki sojan ruwa. Ezekobe ya bayyana haka ranar laraba,July 13 cewa dan danfarar an cafkeshi ne kusan da barikin sojoji ranar alhamis,july 7 da zarginshi na damfarar yan kasa na kudin har N330,000.Mr Pius yace yadai karbi kudi N50,000 a hannu daga mutanen da ya ma alkawalin ze taimaka masu da samun aikin sojan ruwa.
Daraktan sadarwar yace bincike ya nuna wadanda aka damfarar suna cikin mutanen da ake tantancewa na shiga aikin sojan ruwa,bugu daa kari sijojinmu dake (ODS)sun kama wani Prince Moses Ushi A karama hukumar Ughelli ta arewa,jahar Delta.An kama ushi ranar laraba,july 6 a kan zargin da ake mai nayin sojan gona a matsayin sojan ruwa.
KU KARANTA : Buhari yayi magana ga sojin Kasa a Jihar Zamfara
Abubuwan da'aka samu a gurin yan danfarar sun hada da Bindigar roba,hular soja,gajeren wandon soja,da T-shirt ta soja da photocopy katin shaida da alamar doka ta hanaa giftawa ta gaban gidanshi. Dan haka sojojin ruwa na kasa sun gargadi al'umma kasar nan da su kiyaye daa yaan danfara masu cewa zasu taimakesu gurin samun aiki.
Asali: Legit.ng