Yadda yariman Dubai yake gudanar da rayuwa mai tsada

Yadda yariman Dubai yake gudanar da rayuwa mai tsada

Hamdan bin. Mohammed Al Maktoum, shine da na biyu wajan sheikh Mohammed bin Rashid Al Maktoum, shima gwani ne wajan hawa shafukan sada zumunci wanda ake hadashi da Disney's Aladdin.

Yadda yariman Dubai yake gudanar da rayuwa mai tsada

Shidai aka zaba a matsayin yarima bayan kin amincewa da yayansa Rashid bin Mohammed da akayi a shekarar 2008, inda daga bisani ya juya harkar jarida a matsayin abunda yafi so.Hamdan yashiga jerin samari masu yawo a duniyar sararin sama, kuma har ila yau ya shahara a wajen taimakon marayu dakuma gajiyayyu.

Har ila yau Hamdan yayi rubutu a littafin fazza wanda ake rubuta abubuwa masu mahimmanci musamman ga masu yawon Bude ido, kuma yana da mabiya a instagram sama da mutane miliya 3.7. Sheikh din dai ya Gama makarantar kudi ta Rashid dake dubai, Bayan nan ya shiga daya daga cikin manyan jami'an masu tsada a uk_Royal military academy sandhurst.

A taikace dai yariman yayi karatun sa a makarantar dubai da kuma makarantar tattalin arziki ta landan.  Sheikh Hamdan shine mataimakin chiyaman na majalisar zantarwa.Sannan kuma shugaban majalisan wasanni na kasar dubai, kuma shine shugaba a shashin bincike na marasa lafiya wanda suka samu matsalan kwakwalwa, dakuma taimaka ma kananan yara da samun aikin hannu. Shine dai na bakwai a wajan baban sa, yariman yana harkan kiwo, haka kuma mai martaban yana sha'awan tseren doki, Ya tabacin kyautar zinariya a gasar Asian Olympic.

Hamdan yana kiwon rakumai  inda yake kashe musu makudan kudade. Kuma zai Iya hawa kowane irin abun haya zuwa inda zaije, haka Allah yayi shi.

KU KARANTA : Gaskiyar Maganar Gidajen Janar Buratai da ke Dubai

Yariman kasar dubai din dai bai tsaya a harkar kasuwancin dubai dinba, yana kuma taimakama marasa karfi akai akai. Hamdan bin Mohammed yana sha'awan wasa Sosai a zuciyarsa.Sheikh Hamdan bin mohammed yana sha'awan wasa Sosai a zuciyarsa, kuma yana son kiwon tsintsaye. Ya taba zuwa uzbekistan domin halartan taron masu kiyon tsuntsaye. Haka kuma yana sha'awan daukan hotuna harma yakan bada shawara a shafinsa na yanar gizo game da daukan hoto. Yafi amfani da keke alokacin dayake tafiya.Yana kuma sha'awan yawo a karkashin ruwa, kuma yana sha'awan kama kifaye.Wannan shine yariman dubai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel