Chelsea Sun yarda da Biyan kudin Dan Wasan Leceister city

Chelsea Sun yarda da Biyan kudin Dan Wasan Leceister city

-Kante yana kan hanyarshi ta zuwa Stamford Bridge.                                    

-Blues sunyi rohoton yarjejeniyar sayen dan wasan France.                                   

-Dan wasan ance yaki amincewa da sabon kwantaragin da kungiyar shi ta taya mashi.    

Chelsea Sun yarda da Biyan kudin Dan Wasan Leceister city
N'Golo Kante

   

Akwai rohoton daa aka samu cewa chelsea taa yadda da ta biya £29.1m kimanin (N11bn) ga kungiyar Leceister city dan sayen dan wasan tsakiya N'Gole Kante. Daily telegraph UK ta bayyana mana dan wasan tsakiya dan asalin france yaki amincewa da saabon kwantaragin da da kungiyarshi ta taya mashi wanda ya hada da kudin albashi £100,000 a sati,duk da ya ga kungiyar tana shirye da ta ba shi tayi mai tsoka dan ya tsaya kungiyar.

Claudio Reneiri ya roki yan wasanshi dasu tsaya su kara ko daa kakar wasa mai zuwa,sai dai Leceister suna kokarin suga dan wasan da aka saya £5.6m daga kungiyar Caen shekarar da ta gabata be bar kungiyar ba.

A shekara 2015/2016,Kante ya taka rawar gani,sannan kokarinshi da kwazonshi ya taimaki kungiyar lashe premier league kuma ya taimaka gurin rike Kungiyar har satin karshe na kakar, Kante yana kokari wurin tsaron tsakiya,kuma yana kokarin tsaya gurin da ya dace kuma yana kokarin tafiya da kwallo gaba.

KU KARANTA : ISIS ta fille kawunan shahararrun yan wasan kwallo 4

Ankara bayyana cewa sabon kocin  chelsea Antonio Conte ya matsu da yasamu dan wasan na tsakiya.

 

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel