Allura ta tono garma a Enugu

Allura ta tono garma a Enugu

-Binciken ya nuna cewa masu sarautar gargjiya na da hannu a hare-haren Fulani makiyaya a jihar

-Wani jami’in gwamnati ya bankado irin rawar da masu sarautar ke takawa da ya asassa rikicin

Allura ta tono garma a Enugu

An zargi wasu masu rike da sarautar gargajiya a jihar Enugu da hannu a kase-kashen da Fulani makiyaya suka yi a jihar Enugu, ta hanyar karabar haramtaccen haraji a hannun Fulanin.

KU KARANTA: Makiyaya sun hallaka mutane 81 a Benue

Shugaban riko na karamar hukumar Uzo-Uwani Cif Coronel Onwabuya ne ya bayyana cewa wasu masu sarautar da gargajiya ne na yakin suka sa wa makiayayn harajin kiwo a yankunan da ke karakashin mulkinsu.

Allura ta tono garma a Enugu
Daya daga gidajen da aka kona a Ukpabi Nimbo, jihar Enugu. Photo: Michael Obasa

Onwabura na magana ne a a ranar Litinin 11 ga watan Yuli a gaban wani kwamitin bincike na shari’a da gwamnati ta kafa don bin didigin kashe-kashen da aka yi a Nimbo. Owubura ya ce harajin da suke biya ne ya ba maharan karfin gwiwar kai harin a kan kauyukan da su ke zuwa kiwo.

Shugaban rikon ya ci gaba da cewa, saboda yadda aka mayar da Fulanin kamar saniyar tatsa, kan yadda masu sarautar ke karbar kudi, da ma wasu mutanen gari a hannun makiyaya kafin a bar shanunsu su yi kiwo ya kai matuka, wanda kuma hakan haramun ne a hukumance.

Allura ta tono garma a Enugu

Hirar sa da jaridar Daily Trust Cif Onwubura ya ce, wani lokacin Fulanin kan ankara cewa wasu mutane daban suka ba kudin ba wadanda suka dace ba, amma babu yadda za su yi, domin a cewarsa ya yi mu’amilla da Fulanin a lokuta da dama, kuma ya sanar da hukumomin tsaro labarin kai harin kwanaki uku kafin afkawa kauyen Nimbo, domin a cerwarsa, ya ga sansanin maharan a kauyen Ameke.

 

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng