Rundunar soja ta kai wa mayakan Bokoharam hari

Rundunar soja ta kai wa mayakan Bokoharam hari

Jiragen yakin rundunar sojan Najeriya da na Chadi tare da sojojin kasa sun yi nasarar kawar da wani hari da mayakan Bokoharam ta kawo a Kangarwa Arewacin jihar Borno a ranar litinin 12 ga watan Yulio.

A cewar mai rikon mukamin daraktan mu’amala da jam’a na rundunar sojan kasa Kanal Sani Kuka-sheka Usman, an hallaka mayakan Bokoharam da dama a wani gumurzu da aka fara tun kusan karfe 6:30 na yamma, inda aka yi ding rowan harsahi tsakanin runudunar sojan bataliya ta 119 da kuma yan ta’addan.

Rundunar soja ta kai wa mayakan Bokoharam hari

Usman yace sojoji 2 ne suka rasa rayukansu, inda 7 suka samu raunuka. Ya kara da cewa “saboda yanayim gani mara kyau, ba zamu iya tantance yawan yan Bokoharam da muka kashe ba” ya karkare da cewa sun kwashe gawawwakin sojojin da aka kashe da kuma wadanda suka jikkata daga filin daga, inda kuma rundunar take gudanar da zagayen bayan hari.

A wani lamari mai kama da wannan, laftanar janar Tukur Buratai shugaban rundunar sojan kasa

Ya tabbatar da cewa rundunar Hadaka ta kasashen tankin tefkin chadi ta fatattaki ragowan yan Bokoharam zuwa kan iyakokin kasarnan. A cewar Buratai a sa’ilin da yake yin jawabi gay an jarida ya a garin Damaturu bayan ya ziyarci mataimakin gwamnan jihar Yobe wanda ya wakilcin gwamna Ibrahim Gaidam, a yanzu haka yan ta’addan suna boye a kan iyakar Najeriya da Nijar, Chadi da Kamaru. A wani cigaban kuma jami’an tsaro sun cafke wasu yan kungiyar Bokoharam a Legas inda aka kama daya yana buya a cikin coci.

A labarin da jaridar Vanguard ta samo, tace kungiyar yan kato da gora mai suna civilian JTF ta cafke 6 daga cikin yanta’addan a sashi daban daban na na birnin. An ruwaito cewa tun bayan ire iren harin da rundunar soja ke kai ma yan Bokoharam a cikin jihar Borno ba kakkautawa, hakan yayi sandiyyar tserewarsu daga garuruwan Bama, Baga, da Konduga.

Asali: Legit.ng

Online view pixel