Zaben Edo: INEC ta amince da Ize-Iyamu a matsayin dan takaran PDP
Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta INEC ta amince da Osagie Ize Iyamu a matsayin halattaccen dan takaran PDP da zai shiga zaben gwamnan Edo da zata gudanar.
Mataimakin darektan wayar da kan masu zabe da sadarwa na hukumar INEC Nick Dazang ya fayyace haka a wata hira da yayi hukumar dillancin labarai ta kasa a ranar talata 12 ga watan Yulio a Abuja.
Dazang yace amincewar da hukumar tayi wa Ize-Iyamu dan bangaren PDP da Makarfi ke shugabanta ya biyo bayan hukuncin da wata kotu ta fitar akan tirkatirkan. Yace “hukumar ta amshi sunan dan takaran daga hannun bagaren da Makarfi ke jagoranta saboda kotu ta yi umarni da INEC ta amince dad an takaransa. “abu na biyu kuma, idan zaku tuna, zaben cikin gidan da ya makarfi ya shirya ne kawai INEC ta sa ido a kai”.
Jam’iyar PDP ta dade tana fama da rigimar cikin gida, inda bangarori biyu ke ikirarin shugaabancin ta.
Bangaren da Ali Modu Sheriff ke wakilta ta tura sunan Mathew Iduoriyekwemwen a matsayin dan takaransa bayan bangaren da Makarfi ke jagoranta ta gabatar da sunan Ize-Iyamu. Bangaren Makarfi da ta samu goyon bayan dukkanin rassan jam’iyar, ciki hard a kungiyar gwamnonin PDP da kuma majalisar amintattun jam’iyar ta gabatar da zaben cikin gida a ranar20 ga watan Yunia garin Bini inda kuma aka zabo Ize-Iyamu a matsayin dan takaranta. Daga bisani kuma a ranar 29 ga watan yuni bangaren Sheriff ta zabi Iduoriyekwemwen a wani zaben cikin gida da ta gudanar ba tare da sa idon hukumar zabe ba.
A ranar 4 ga watan yulio ne dai wata kotun tarayya dake zaune a garin fatakwal ta yanke hukuncin cewa taron jam’iyar da ya gudana a ranar 21 na watan Mayu wanda ya tsige Sheriff kuma ya nada yan kwamitin wucin gadi a matsayin sahihin ne domin a kafa shi yadda ya kamata.
A ranar 21 ga watan mayu ne shugabancin PDP ta fatattaki Sheriff da sauran yan kwamitin zartarwa na jam’iyar a taron jam’iyar da ya gudana a garin fatakwal. Taron kuma ya amince da nadin wani kwamitin riko na mutane 7 da Makarfi zai jagoranta.
A yayin yanke hukuncin, mai shari’a Abdullahi Liman ya yanke cewa nadin kwamitin riko da zai tafiyar da al’amuran na kan ka’ida, kuma yayi daidai da kundin tsarin mulkin PDP.
Asali: Legit.ng