Amurka za ta gabatar da shaida kan ‘yan majalisa
-‘Yan majalisar da suka yi abin kunya a Amurka za su bayyana a gaban kwamitin da’a na majalisar Wakilai
-Jakadan Amurka mai barin gadon ya shirya gabatar da faifan bidiyo kan ‘yan majalisar da ake zargi
-Za’a ba ‘yan majalisar damar kare kan su
An shirya bayyanar ‘yan majalisar wakilan da ake zargi da aikata abin kunyar neman yin lalata a yayin da suke ziyarar aiki a Amurka, a gaban kwamitin da’a na majalisar wakilai, a ranar Alhamis 14 ga watan Yuli.
KU KARANTA: Dogara ya koka da rashin shugabanci nagari
A cewar jaridar This day, ana shirin sauraron batun a bainar jama’a a ranar Alhamis din nan, bayan da jakadan Amurkan a Najeriya James Entwiste ke shirin ganawa da shugaban majalisar Wakilan a kan zargin da ake yiwa ‘yan majalisar su uku.
Ana zargin ‘yan majalisun ne su 3 da aikata abin kunyar ne a lokacin da suke wata ziyarar aiki a karkashin wani shiri na samar da shugabanci nagari a garin Cleveland, da ke jihar Ohio a Amurka a tsakanin ranakun 7 zuwa 13 na watan Afrilu. ‘Yan majalisar na cikin ayarin ‘yan majalisar wakilan su 10 wadanda suka kai ziyarar.
A cewar shugaban kwamitin da’a na majalisar Nicholas Ossai, ba za su gayyaci masu otal din da abin aka aikata abin kunyar ba don bayar da shaida, saboda jakadan kasar ne ba kawo karar ‘yan malajisar ta hanya wasika zuwa ga shugaban majalisar wakilan, sannan ya kara da cewa kwamitin zai yi bincikensa a bayyana ne.
Asali: Legit.ng