Buratai: anyi bikin Sallah na daban

Buratai: anyi bikin Sallah na daban

A satin da ya gabata ne hukumar soji ta watsa hotunan shugaaban hafsan sojan kasa na Najeriya Tukur Buratai a yayin shanruwa da yayi da wasu rundunonin yaki a arewa maso gabas.

A wannan kasidar, Philip Agbese shugaban kungiyar ‘Stand up Nigeria’ wata kungiyar sa kai ya yabawa Buratai da irin wannan hali na sa wandan ya bayyana shi a matsayin shugaban da ya salwantar da kai wurin bautan kasarsa da kuma kokarin sanin abin dake faruwa a filin daaga da kankin kansa.

Buratai: anyi bikin Sallah na daban
Buratai a yayin shnaruwa da sojoji a filin daaga

A daidai lokacin da ilahirin jama’a musulman duniya ke bikin karshen watan Ramadan, gwaraza guda biyu a bangarorin duniya guda biyu sun aika sako zuwa ga yan ta’adda dake fadin duniya cewaba wasu tsurarun yan ta’adda basu isa su hana zamn lafiya a duniya ba, suna kashe raid a sunan addinin miliyoyin mutanen dake gudanara da bikin sallar Idi a karshen Ramadan. Shugaban rundunar sojan kasa na Pakistan Janar Raheel Sharif yayi sallar idi tare da rundononin soja a filin daaga na sashin arewa da kudancin Waziristan, yayi sallar idi a shawwal daga bisani ya ziyarci wasu rundononin dake wasu yankunan.

Kafin ziyarar ta Sharif ga sojojinsa, a nan gida Najeriya, shima shugaban sojan kasa na Najeriya Janar Tukur Buratai yayi buda baki tare da sojojin tundunar bataliya ta 103 a dajin konduga dake jihar Borno a ranar Litinin 4 ga watan yuli. Wannan cikin irin ziyarar aiki ne da yake kaiwa tashohin soja a arewa maso gabas, wanda cigabane da hidimar bikin zagoyawar ranar sojan kasa na 2016, janar Buratai ya ziyarci rundunan sojan bataliya ta 119 dake karkashin biget na 7 dake garin Kangarwa. Sa’annan ya shiga Konduga, Dikwa har ma da garuruwan Najeriya dake iyaka da Kamaru, Chadi da Nijar inda yan ta’adda ke fakewa, duk da irin matsalar tsaro da ake fama dashi da kuma sanin cewa yan ta’adda ba zasu bari irin wannan ziyara ta wuce ba face sun kai hari.

Irin wannan aiki ne ya tabbatar me yan Boko haram cewa zamanin da suke fuskantar sojojin Najeriya ba kayan aiki ya wuce kamar yadda ziyarar Shugaban sojan kasa na Pakistan zai nunar ma yan Taliban cewa karfin iko na kasar na nan ya mamaye ko ina. A Najeriya kuwa, an wuce zamanin da ake sa ido a yakin da akeyi daga cikin dakunan alfarma. Shuwagabbannin hukumar Soji na sake salon yaki tare da rundunoninsu daga cikin dazuka. A yanzu hukumar sojan kasa na samun labarai ne da dumi duminsu tun da a gabansu ake yi, kuma suna samun daman magance matsaloli nan da nan.

Wannan irin sadukarwan na Buratai da kuma jami’ansa da sojojinsa don ganin samun zaman lafiya a kasa ba zai misaltu ba. Don haka ya kamata a lura wannan na daya daga cikin dalilan da yasa yan Najeriya suka tashi tsaye wajen kareshi a kowani lokaci. Wandanda ko suke son bata mai suna su sani cewa irin shugabancin sa ne ya janyo mai daukaka kuma yasa rundunonin soja suka gay a kamata su bautawa kasarnan. Haka kuma irin wadannan halayyansa ne suka sa jama’a fararen hula suka aminta dashi, yasa suke iya gane duk wani karya da aka yi masa.

Abin la’akari ne irin wannan amintaccen shugaban sojan kasa, shugaban zai iya tunkaho da irin wannan bikin Sallah da akayi shi lafiya ba tare da tashin bamabamai ba kamar yadda aka saba. Alama deke nuna cewa wata rana za’a mu kwana lafiya mu tashi lafiya ba tare da wani fargaba ba kamar yadda ake samu a sauran sassan duniya. Duk dacewa kowa ya san cewa yawancin tashin tashinan ma siyasa c eta kawo shi, yan Bokoharam sun  kai wasu harehare bayan ziyaran Shugaban sojan duk don su nuna alamar ba’a samu wata sauki ba kamar yadda ake fada. Amma abin dubawa anan shine irin fatattakarsu da jami’an soja sukayi inda da dama daga cikin su suka rasa rayukansu, wasu kuma suka sha da kyar.

Wanna na daga cikin bangaren da ya kamata janar Buratai dole yayi gyara, a duk lokacin da shi ko wani babban Jami’i ya kai ziyara bakin daaga, dole ayi shirin ko-ta-kwana don kare kowani irin hari da yan ta’addan zasu kai. Ghandi na Indiya yayi gaskiya sa’adda yace “kyauta halin mai karfi ne, mai karfi ne kawai zai iya bayarwa musamman ma idan bai bukatan a biyashi”, wannan ya bayyana yadda Buarati ke gudanar da al’amuransa. A yayin da waus ke kwashe kudaden sojoji da kuma kudaden siyan makamai, shiko ya sadaukra da kansa ne. Buratai yana sa kansa cikin irin halin da sojojinsa suke ciki, babu kyatar da ta wuce sadukar da kai wuri bauta wa kasa.

Wannan madubin dubawa ne game da yadda shugaban sojan kasa yake aikata abin da yake fadi a filin daaga. Ba ma wait a baangaren matsayinsa a Soja, wani halin nasa shine taimakon mutane, wanda yake yawan nunawa ba tare da nuna bambamcin kabila ko addini ba. Abokin talaka ne, a kullum yana fautuka a bayyane ko a boye don ganin sun samu sauki. Haka kuma yak gudanar da al’amuran da suka shafi alabashi da alawus din sojojinsa da na iyalansu.

Da wannan halin nasa ne yasa duk da harsashen da ake harbawa, amma yake samun lokaci yan ziyartar sojojinsa akai akai har ma yaci abincinsu. A yayin da zaka ga tsananin soyayyar da yake nunawa sojojinsa wanda hakan zai basu kwarin gwiwar cin yakin da suke yi da ta’addanci, kazalika zamu iya fahimtar sa a matsayin wani shugaban soja dake son ganin an baiwa dukkan sojoji hakkinsu a yayin da suke yi wa kasarsu hidima. Zamu iya tuanwa anyi kokarin gaske wajen tayar da tarzoma tsakanin sojojin ta hanyar hada labarum kanzon kurege cewa wai ba’a biyan su albashunsu da kuma alawus alawus

Amma da irin halayen da Buratai ya nuna, ba mamakin bacewar irin labarukan da ke samu a baya na sojoji dake harbin kwamandodinsu tun hawar kujeran shugaban sojan kasa. Da shi kam Sojan kasa ta Najeriya ta samu kwatankwaci shuagaba Buhari wanda dabi’unsa kawai suna baiwa yan kasa kwarin gwiwar su rungumi canji, duk da cewa akwai sadukarwa na musamman da kowa zai yi. Fatan da ke yi shine idan karshen watan Ramadan mai zuwa ya zagayo, kwarin gwiwar da Buratai ya baiwa sojoji ya sa an karar da yan Bokoharam gaba dayansu, saboda dubunnan yan gudun hijira su yi bude baki a gidajensu.

Agebese shine shugaban wata kungiyar sa kai mai suna Stand Up Nigeria na kasa, dake zaune a kasar Birtaniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng