Sheik Dahiru Bauchi ya kara aure

Sheik Dahiru Bauchi ya kara aure

Fitaccen malamin addinin musuluncin nan Shehi Dahiru Usman Bauchi ya kara aure shekara 68 tun bayan ya auri matarsa ta fari.

Sheik Dahiru Bauchi ya kara aure
Shehi da Matarsa

Shi dai malamin dan Shekara 89 a rayuwa kuma jagoran darikar tijjaniya a Najeriya yayi sabuwar amarya wadda take ya ce ga shahararren malamin nan kuma Kalifan Tijjaniyya Shehi Ibrahim Inyass.

 

Jaraidar Hausa ta Rariya ta ruwaito cewa Sheikh Baba Laminu Inyass ne daura auren a can Kaulaha, kasar Sanigal.

 

Shehi Dahiru Bauchi shi ne mataimakin shugaban kwamitin fatawa na kungiyar harkokin musulunci ta kasa gaba daya, Shehin malamin yayi aurensa na fari a shekarar 1948 kuma yana da yaya 61, jikoki da tattabakunne da dama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel